Zaɓen Ekiti 2026: Shettima ya nemi al’ummar jihar su sake zaɓen Oyebanji

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga al’ummar Jihar Ekiti da su sake zaɓen gwamna mai ci, Biodun Oyebanji, a zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin babban taron yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC da aka gudanar a Ado-Ekiti, babban birnin jihar, inda ya wakilci Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce tikitin Oyebanji da mataimakiyarsa, Hajiya Monisade Afuye, ya haɗa gogewa, daidaito da kuma ci gaba, yana mai jaddada cewa sake zaɓensu zai tabbatar da dorewar zaman lafiya, ci gaba da walwalar al’ummar jihar.

A cewarsa, zaɓen ba wai kawai wata gasa ce ta siyasa ba, illa wata dama ce ga al’ummar Ekiti su ci gaba da gina makomarsu ta hanyar ci gaba da ayyukan da gwamnatin Oyebanji ta fara.

“Ci gaba da bai wa Oyebanji dama ba wata alfarma ce ga mutum ɗaya ba. Zuba jari ne a zaman lafiya, ci gaba da makomar Ekiti,” inji Shettima.

Mataimakin shugaban ƙasar ya yaba da yadda dimbin jama’a suka halarci taron, yana mai cewa hakan ya nuna goyon bayan da mutanen jihar ke bai wa APC da gwamnatin tarayya.

Ya bayyana Oyebanji a matsayin shugaba mai tawali’u da sanin ya kamata, wanda ya mayar da hankali wajen yi wa jama’a hidima maimakon siyasar rikici.

“Ya yi aiki domin haɗa kai, ƙarfafa amana da kuma tabbatar da cewa gwamnati tana amfanar da talaka, manomi, malamai, ma’aikata da sauran jama’a,” inji shi.

Shettima ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin Ekiti wajen bunƙasa ci gaba, samar da damarmaki, ƙarfafa tsaro da habaka tattalin arziki.

A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana Oyebanji a matsayin ɗaya daga cikin gwamnoni mafi kusanci da majalisar dokoki a Najeriya.

Ya ce gwamnan ya yi ayyuka masu gamsarwa kuma ya cancanci sake samun wa’adin mulki.

“Idan kun je rumfunan zaɓe, ku zaɓi alamar tsintsiya. Yin haka yana nufin ku ka zaɓi ci gaba da kyakkyawan shugabanci a Ekiti,” inji Akpabio.

Shi ma Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yaba da salon shugabancin Oyebanji, yana mai cewa ya dace da manufofin APC.

Ya yabawa gwamnan kan nasarorin da ya samu a fannonin ilimi, lafiya da gine-ginen more rayuwa.

Tun da farko, Gwamna Oyebanji ya gode wa Shugaba Tinubu da Mataimakin Shugaban ƙasa Shettima bisa goyon bayan da suke bai wa jihar tun bayan hawansu mulki a shekarar 2023.

Ya kuma gode wa al’ummar Ekiti saboda amincewar da suka ba shi, tare da roƙonsu da su guji tashin hankali kafin, lokacin da bayan zaɓen ranar 20 ga Yuni.

“Mun yi iya ƙoƙarinmu wajen cika alƙawuran da muka ɗauka a gare ku. Ina roƙonku ku fito ku kaɗa ƙuri’arku cikin lumana domin ci gaba da aiwatar da ajandar ci gabanmu,” inji gwamnan.

Kafin halartar taron yaƙin neman zaɓen, Shettima ya kai ziyarar girmamawa ga Ewi na Ado-Ekiti, Oba Adeyemo Adejugbe, inda ya yaba da rawar da sarakunan gargajiya ke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.

Haka kuma ya gana da mambobin Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Ekiti, inda ya tabbatar musu da goyon bayan gwamnatin Tinubu ga cibiyar sarauta.

A nasa bangaren, shugaban majalisar sarakunan da kuma Ogoga na Ikere-Ekiti, Oba Adu Adejimi Alagbado, ya yaba da ziyarar Mataimakin Shugaban ƙasar, yana mai cewa hakan wata alama ce ta ƙaunar da Shugaba Tinubu ke yi wa al’ummar Ekiti.

Ya kuma yi alkawarin cewa sarakunan gargajiya za su ci gaba da mara wa gwamnatin tarayya da ta jihar baya domin tabbatar da ci gaba da zaman lafiya a jihar.

By ukarofi

Leave a Reply