Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya yi barazanar tsige duk wani shugaban ƙaramar Hukumar da ya gaza tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a yankinsa a babban zaen shekarar 2027.
Nwifuru ya bayyana hakan ne a Abakaliki, babban birnin jihar, yayin rantsar da sabbin shugabannin ƙananan Hukumomi 13 da mataimakansu.
Gwamnan ya ce duk shugaban ƙaramar Hukumar da ya kasa tabbatar da nasarar APC a yankinsa za a tsige shi daga muƙaminsa tare da maye gurbinsa da kansila.
“Duk shugaban da ya kasa lashe ƙaramar Hukumarsa za a tsige shi, a maye gurbinsa da kansila,” inji Nwifuru.
Ya ce bai kamata shugabannin ƙananan Hukumomin su yi sakaci ba ko su bar jam’iyyun adawa su samu damar kare yankunansu, yana mai umartar su da su yi aiki tuƙuru domin tabbatar da gagarumar nasarar APC a zaen 2027.
Nwifuru ya kuma buƙaci shugabannin su yi iya ƙoƙarinsu domin APC ta samu kashi 100 bisa 100 na ƙuri’un yankunansu, tare da gargaɗin kada su bari jam’iyyun adawa su ƙara ƙarfi a ƙananan Hukumomin da suke jagoranta.
Gwamnan ya kuma shawarci shugabannin ƙananan Hukumomin da mataimakansu su yi aiki tare cikin haɗin kai tare da guje wa rikici da gasa a tsakaninsu.
Ya buƙaci mataimakan shugabannin su riƙa bai wa shugabanninsu cikakken goyon baya, tare da guje wa sauraron jita-jita ko maganganun da za su iya lalata dangantakarsu.
Nwifuru ya ce kyakkyawan aiki da gudanar da muƙami yadda ya kamata na iya buɗe wa mutum ƙofofin samun manyan mukaman siyasa a gaba, inda ya kawo Mataimakiyar Gwamnansa a matsayin misali.
Da yake magana a madadin sauran sabbin shugabannin ƙananan Hukumomin, Shugaban ƙaramar Hukumar Afikpo, Timothy Nwachi, ya gode wa gwamnan da shugabannin jam’iyyar APC bisa damar da aka ba su ta yi wa al’umma hidima.
Nwachi ya yi alƙawarin cewa za su yi aiki domin tabbatar da amincewar da aka yi da su, tare da tabbatar da cewa APC ta samu gagarumar nasara a zaen 2027.
Daga cikin sabbin shugabannin ƙananan Hukumomin akwai Osborne Umahi, ɗan Ministan Ayyuka, David Umahi, da Chidi Nwode, wanda ke da alaƙar iyali da matar Gwamna Nwifuru.
