Ƙungiyar iyayen yara ta yaba wa ƙoƙarin Kwalejin Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu

Daga MUHAMMADU MUJITABA

Shugaban ƙungiyar iyayen yara da malaman makaranta na rukunonin makarantun Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu, Alhaji Abubakar Jibrin Madigawa ya yaba wa wannan makaranta ne kan shirya wa ɗalibai 180 walimar kammala makarantu sakandire da firamare, a makarantar ƙarƙashin shugabancin babban jami’in tsare-tsare na makarantun khalifa, Malam Ibrahim Bashir Dodo kan ƙoƙarinsa na tsara irin wannan walimar irinta na farko don inganta walwala da ƙwaƙalwar ɗalibai da ƙarfafa musu gwiwa bayan kammala karatun na wannan lokaci.

Shugaban ƙungiyar iyayan da malaman makarantar Abubakar Jibrin Madigawa ya bayyana haka ne a lokacin bikin walimar da makaranatar khalifa Isyaka Rabiu ta gabatar a harabar makarantar da ke Kano a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

Shi ma babban jami’in makarantar, Malam Ibrahim Bashir Dodo ya bayyana cewa, babban dalili na shirya wannan walima ga ɗalibai 180 na makarantar shi ne kawar da matsaloli da ke faruwa a Kano da sauran wurare bayan kammala sakandire da ɗalibai ke yi na bikin candy wanda abun ke ba al’umma tagari matsala da ciwon kai da takaici sakamakon yadda yara ɗalibai suke abubuwa marasa kyau kamar yaga rigona, shaye-shaye, iface-iface, maganganun batsa da sauran abubuwa na nuna rashin tarbiyya da sunan murnar kammala makaranta wanda wannan ba ƙaramar matsala ba ce a cikin alummar mu musulmi kuma Hausawa masu nagarta da sanin yakamata a ce wannan na faruwa abun damuwa ne, don haka mu ka hana su kuma mu ka shirya musu wannan walima don ƙarfafa gwaiwa gare su.

Har ila yau malam Ibrahim Bashir ya ce, kuma suna alfahari da godiya ga malaman mu kan yadda ɗaliban su suka kasance haziƙai akan duk wani fanni na karatun su tunda ga kan masu kimiyya, Turanci, Art da kuma Larabci duk a makarantun sakandire yara suna nuna bajinta wanda a ko’ina cikin duniya za su kare takardun su da kimar wannan makaranta.

A ƙarshe dai malam Ibrahim Dodo babbab jami’ da Malam Tukur shugaban makaranta sun ya yaba wa ɗaukacin iyalan Khalifa Isyaka Rabiu tundaga kan Khalifa Rabiu Nafiu, Alhaji Nura, Alhaji Mustapha Rabiu da dai sauran su maza da mata na iyalan Khlifa kan tsayawa ilimi da hidimar jama’a sai Kuma Hajiya Asabe Sani Ƙofar Naisa Daraktan Ilimi ta shirya Dala, Farfesa Sani Musa Ayagi ɗaya daga cikin tsofafin ɗalibai makarantar kan namijin ƙoƙarinsu ga makaramtar da harkar ilimi bakiɗaya.