Ko mun san ma’anar Tarbiyya?

Assalamu alaikum. Tarbiyya kalma ce da ta samo asali daga Harshen Larabci. Tarbiyya wani ɓangare ne ko jigo a rayuwar ɗan Adam. Manufar Tarbiyya shine, gina mutum ya tashi cikin kyawawan halaye da ɗabi’u.

Tarbiyya a Hausa na nufin, cikakken Mutum wanda ya ke da halaye da ɗabi’u masu inganci. Akan alaƙanta mutum mai nutsuwa, mai girmama na gaba, mai sanin ya kamata, mai iya kalami, mai kyakkyawar mu’amula da suna mai Tarbiyya. A taƙaice, mutum na samun cikakkiyar daraja da mutumtaka a idon jama’a idan ya kasance mai Tarbiyya.

Jigon masu bada tarbiyya ga ɗan Adam su ne; Iyaye da Al’umma. Yayin da a ɓangare guda ake alaƙanta masu ɓata tarbiya da; baragurbin abokai da kuma Kwaikwayo daga abubuwan da ake kalla na yau da kullum wanda daga bisani sai mutum ya fara kwaikwayon ko aiwatar da abinda ya ke kalla, kamar daga fina-finai, waƙoƙi, raye-raye da sauransu.

Manazarta sun zayyana hanyoyi da matakan bada tarbiyya kamar haka; Nuni, Lura ko Kula, Umarni da kuma Hani ko Kwava.

Taɓarɓarewar tarbiyya, wani babban ƙalubale ne da ake kokawa akansa a halin yanzu. Al’amarin yayi tsamarin da iyaye da kansu na kokawa kan lalacewar tarbiyyar ’ya’yan da suka haifa. To ko ina gizo ke saƙar?

Da dama su na alaƙanta hakan da sakacin iyaye wajen ɗabbaƙa waɗancan matakai guda huɗu wato; Nuni, Lura/Kula, Umarni, Hani/Kwava.

A hannu guda kuma, wasu na alaqanta taɓarɓarewar tarbiyya da wanzuwar baƙin al’adu da cuɗanya da mutane masu ƙarancin tarbiyya.

Yayin da wani ɓangaren ke alaƙanta hakan da yawaitar tashoshin talabijin da wayoyin hannu wanda ke ɗauke da manhajoji da shafuka iri-iri wanda sukan taka muhimmiyar rawa wajen taɓa tarbiyya, wanda hakan ya sa a halin yanzu gwamnati ke neman hana ’yan shekara ƙasa da 18 mallakar layin waya.

Ra’ayoyin ’yan Nijeriya ya bambanta game da yunƙurin Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) na haramta wa masu ƙasa da shekara 18 sayen layin waya.
’Yan Nijeriya sun bayyana ra’ayoyinsu mabanbanta game da matakin na NCC, wanda zai haramta wa kamfanonin sadarwa yi wa masu ƙasa da shekara 18 rajistar mallakar layin waya nan gaba.

Dukka waɗannan na samun wajene su yi tasiri wajen gurvata tarbiyyar yaro idan iyaye suka yi sakaci wajen bibiyar yadda ‘ya’yansu ke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Akwai buqatar iyaye su zage damtse wajen dawo da tarbiyya yara kan hanya, ta hanyar; Nuna musu abinda yake dai-dai da savanin haka, ka kuma kasance madubin da yaranka zasu yi kwaikwayo daga gare ka, da lura akan waɗanda suke mu’amula da su da bibiyar al’amuran da suke gudanarwa da wayoyinsu na hannu kasancewar kaso mai yawa na abubuwan rashin gaskiya na faruwa ne ta hanyar amfani da wayar hannu, na ƙarshe kwavarsu kan wani abu da suke ba dai dai ba.

Daga Mustapha Musa Muhammad a Kaduna, 08168716583.

Rashin mazan aure ya aru a Nijeriya ne saboda tsadar rayuwa

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Wasiƙata ta yau za ta tafi ne kai tsaye ga yadda rashin mazan aure ke qara ƙaruwa a Nijeriya sanadiyyar tsadar rayuwa. Nijeriya tana da yawan al’umma, musamman matasa, matashi shine mutumin da yake tsakanin shekara 15 zuwa 35. Bincike ya nuna cewa, fiye da kaso 70 na ‘yan Nijeriya matasa ne. Waɗannan matasa sune kayan aikin cin zaɓe a qarshen kowacce shekara huxu. Tabbas, dukkan zaɓukan da aka yi a Nijeriya sun tabbatar da haka.

Alƙaluman ƙididdiga sun nuna cewa, Nijeriya wadda ke da yawan al’umma sama da miliyan 206 ta na da matasa miliyan 33, 652, 424 haka ma daga cikin wannan adadin matasa miliyan 13.9 ne ke zaune babu aikin yi kamar yadda Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana wanda hakan ya faru ne a dalilin kasawar Gwamnatoci a matakin Tarayya, Jiha da Ƙananan Hukumomi wajen baiwa matasa gurabun ayyukan yi wanda zai taimaka masu tare da ba su damar zama masu dogaro da kai.

Gaskiyar lamari, da yawa daga cikin matasan Nijeriya suna fama da rashin aikin yi. Mafi yawancinsu suna rayuwa ne tsakanin talauci da gwagwarmayar neman sana’a. Wasu kuma suna da sana’ar amma nauyin iyayensu ya ƙannensu. Rashin tsaro a ƙasar ya yi sanadin rushewar sana’o’in mutane da yawa.

Tsadar aure gagarumar matsala ce mai zaman kanta da ke ci wa ɗimbin matasa tuwo a kwarya. Hasalima a kwanan baya a yayin da hankalin al’ummar ƙasa ya karkata ga zanga-zangar EndSARS, wasu matasa a Sakkwato sun gudanar da ta su zanga-zangar ne ta neman sauƙi da sauƙaƙawa a tsadar aure.

Aure al’adar ɗan Adam ce, har waɗanda ba Musulmai ba. Haka Allah ya tsara rayuwarmu. Wani masanin ɗabi’ar ɗan Adam, mai suna George Peter Murdock ya bayyana cewa, ko ina ana yin aure a duniya.

Nema da rayuwar aure suna da alaƙa da tattalin arziki. Hakan ne ya sa, tashin farashin abubuwa a Nijeriya ya kawo cikas da tasgaro a wajen auren zawarawa da ‘yan mata. Misali, neman aure yana tafiya ne da abubuwa na al’ada, waɗanda su ke cin kuɗi. Lefe yana ɗaya daga cikinsu, wanda akansa, neman aure da yawa ya lalace. Farashin gidan haya ya tashi, ballantana mallakar gida.

Talauci, tashin kayan masarufi da rashin tsaro sun haifar da mace-macen aure barkatai a gari. Matasa sun koma maula don su rayu. ’Yan mata da zawarawa sun rasa miji saboda masu auren nasu ba su da wadata.

Na tattauna da matasa da yawa a garin Kaduna, inda da yawa daga cikinsu suka bayyana min cewa suna son yin auren amma ba su da yadda za su yi. Akwai wani matashin da na zanta da shi inda yake bayyana min cewa, akwai lokacin da yana ji yana gani aka aurar da yarinyar da yake so saboda bas hi da kuɗi, wanda haka ya sanya shi jin cewa a duniya babu wata macen da zai ƙara ƙallafa rai a kanta.

Matasa sun shiga cikin halin ha’ula’I matuƙa a Nijeriya. Mutumin da zai iya zama da mace uku, yanzu bai fi qarfin zama da mace ɗaya ba.

Nijeriya tana buƙatar taron dangi idan ana neman mafita. Dole sai an ajiye adawar siyasa a gefe, an karɓi shawara daga mutanen da su ka cancanta. Mulki ba ƙaramin abu bane, rayuwar al’umma ake tasarifi da ita. Don haka, abun yana buƙatar tunani sosai. Shugaba mai inganci, shi ne wanda ya ke buɗe tunaninsa kafin ya aiwatar da abu.

Daga Alkazeem M. Sharif Alhasan, 08062740226.