Ya kamata gwamnati ta waiwaye mu, cewar ƙungiyar masu sana’ar kifi

Daga MOHAMMED ALI GOMBE

Ƙungiyar masu sana’ar kifi ta Jihar Gombe, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta waiwaye su, ta sa su a cikin waɗanda za su mori gajiyar tallafin da za ta bai wa ‘yan kasuwa duk lokacin da tsarin bada tallafin ya taso nan gaba.

Ƙungiyar wanda a turance, ana kiran ta ‘Nigeria Union Of Fish Sellers’, Gombe State Branch’ wanda kuma mambobin ta sun haura sama da mutum dubu ashirin (20, 000) a duk faɗin jihar , ta yi kukan cewa, tunda ake raba wa ‘yan kasuwa masu sana’o’i iri-iri da ke cikin jihar tallafi ita ba ta taɓa moriyar ko sisi ba.

Alhaji Suleman Bandirawo, shine Mataimakin Shugaban ƙungiyar wanda a tattaunawar shi da wakilin mu a ofishin ƙungiyar dake cikin babbar kasuwar Gombe a makon jiya, ya nuna takaicin shi matuƙa a madadin ‘ya’yan ƙungiyar a kan rashin tuna su da gwamnatin jihar Gombe take yi duk lokacin da ta tsara baiwa ‘yan kasuwa gudunmuwar tallafin bunqasa sana`nar su.

A cewar shi, “masu sana’ar kifi a nan Jihar Gombe, manya da ƙanana, mun haura mutum sama da dubu ashirin da suke cikin jihar, amma abin takaici shine, yadda gwamnati ba ta tunawa da mu duk lokacin da ta tashi bada irin tallafin da ta saba raba wa ‘yan kasuwa da wasu masu sana’o’i daban-daban na cikin jihar, duk da irin alfanun mu wajen bunƙasa tallafin arzikin jihar, ta biyan haraji ga ita Gwamnatin jihar da kuma ƙananan Hukumomin ta.”

Suleman Bandirawo ya qara da cewa, tun da suka fara sana’ar su ta kifi a jihar Gombe fiye da shekaru talatin yau da mutum takwas kacal wata tun kafin a ƙirƙiro jihar ta Gombe a 1996, da membobi sama da dubu ashirin , amma ko sau ɗaya ba su tava samun ko wani irin taimako daga gwamnati ba.

‘’Saboda haka, yanzu muna kira ga wannan gwamnatin ta Maigirma Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ta yi wa Allah da Annabi, ta dube mu da idon rahama, duk lokacin da ta tashi raba wa `yan kasuwa tallafi, to ta samu a ciki, don mu ma ‘ya’yanta ne,” inji shi.
               
Mataimakin shugaban ya yi nuni da cewa, banda tallafi suna da matsalar rashin kayayyakin sana’a kamar motocin jigilar hajar su ta kifi, da rashin ɗakin sanyi domin adana kifi, wato (Cold Room), da kuma rijiyar burtsatse, ya ƙara da cewa, hatta motocin jigalar kifi daga cikin jihar zuwa wasu wurare, duk sune suke tara kuɗaɗe su gudanar.

Alhaji Suleman ya shaida cewa, shekaru biyu da Gwamna Inuwa Yahaya ya yi yana mulki, babu shakka ya yi abin azo a gani a faɗin jihar wajen shimfiɗa ababen ci gaba lungu da saƙo, kuma su ‘yan kifi suna jinjina mishi, suna kuma goyon bayan shi ɗari bisa ɗari, sai dai ya yi maza ya ƙara da cewa , ‘’mu dai baya ga yaba mishi, muna kuma roƙon shi da ya yi mana adalci, ya samu a cikin `yan kasuwan da za a baiwa tallafin gwamnatin shi duk lokacin da ta tashi yin haka.‘’