‘Yan sanda sun fara bincike bayan karɓe iko da ofishin NSCDC da masu haƙar ma’adinai 37 suka rasu a ciki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Neja, ta karɓe iko da gurin da masu gargajiyar haƙar ma’adinai suka rasu a ofishin Hukumar Sibil Difens NSCDC da kuma fara bincike akan al’amarin.

Wannan ya biyo bayan umarnin Sufeto-Janar na rundunar, Olatunji Disu na ta bankaɗo ainihin dalilan da suka sabbaba mutuwarsu da tabbatar da gaskiya da adalci tare da martaba ‘yancin dokar ƙasa ga mamatan.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan Neja ta fitar a ranar Litinin, Kwamishinanta, CP Adamu Elleman ya umarci tawagogin sintiri na Operation Flush da su killace tare da kula da wajen har sai an kammala bincike.

Tuni dai Mataimakin Kwamishinan ‘yan sandan na Reshen Binciken Manyan Laifuka (SCID) a Minna, ya fara bincike domin gano yadda al’amarin ya kasance bisa bayyana ainihin dalilan faruwarsu.

A cewar rundunar, za a gudanar da binciken ne bisa ƙwarewa tare da ƙoƙarin yin nazari akan dukkan bayanan da suka tabbata kan mace-macen.

CP Elleman ya kuma tabbatar wa iyalai da ‘yan uwan mamatan da kuma al’umma cewa rundunar tana gudanar da binciken ne bisa tsarin doka da oda don ganin an yi adalci kan lamarin, yana mai kira a gare su da su kwantar da hankali da cigaba da juriya har zuwa lokacin da za a fitar da sakamakon bincike.

By Babaji

Leave a Reply