Ya kai ɗan uwa ɗan Nijeriya,
Akwai wasu matsaloli da suke shigowa cikin al’umma a hankali, amma idan aka bar su suka yi ƙatutu, sai su zama kamar gobarar da ba ta bambance gida da masallaci, attajiri da talaka, ɗa da uba. Shaye-shaye na cikin irin waɗannan matsaloli. Ba wai kawai yana lalata lafiyar mutum ba ne; yana iya lalata tunaninsa, tarbiyyarsa, dangantakarsa da iyalinsa, sannan ya zama wata ƙofa da wasu laifuka masu tsanani ke shiga.
A yau, idan aka ambaci yaƙi da shaye-shaye a Kano, sunan Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado ya zama baƙon da ba ya ɓoye a cikin wannan magana. A matsayinsa na Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Jihar Kano kan Yaƙi da Shaye-shaye da Abubuwan Maye, Muhuyi ya shiga sahun waɗanda suke ƙoƙarin ganin an tunkari wannan matsala da ƙarfi.
Amma abin mamaki shi ne, yayin da wasu ke kallon wannan yunƙuri a matsayin abin yabawa, wasu kuma suna kallonsa a matsayin wuce gona da iri, ko ma cin zarafin ’yancin ɗan Adam.
To, bari mu tsaya mu tambayi kanmu wata tambaya mai sauƙi: Idan kare al’umma daga masu lalata rayuwarta ya zama wuce gona da iri, to mene ne za mu kira sakacin da zai bar miyagun ƙwayoyi su mamaye matasanmu?
A nan ne nake ganin ya kamata mu daina kallon batun da idon siyasa ko son rai.
Ba a ce duk wanda aka kama da zargin shaye-shaye ya zama mai laifi ba. Ba a ce a take a hukunta mutum ba tare da bin doka ba. A’a. Doka ita ce garkuwar kowa, kuma duk wanda ake zargi yana da haƙƙin a saurare shi, a bincike shi, sannan a gurfanar da shi a gaban kotu idan akwai hujja.
Amma bin doka ba yana nufin jami’an tsaro su zauna suna kallon masu lalata rayuwar matasa ba.
A ’yan makonnin nan, kwamitin na Kano ya gudanar da samame a wuraren da ake zargin an mayar da su cibiyoyin shaye-shaye. A wani samame a Gandun Albasa da Kasuwar Rimi, an kama sama da mutane 30, yayin da aka samu wasu sama da 30 a yankin layin dogo na Fagge, inda aka zarge su da amfani da miyagun ƙwayoyi. Gwamnatin Kano ta ce tana da shirin cire mutum 10,000 daga masu shaye-shaye, masu safarar miyagun ƙwayoyi da ’yan daba daga kan tituna, tare da kai wasu neman gyara, koyar da sana’a da taimaka musu su koma rayuwar yau da kullum.
Wannan muhimmin bayani ne: aikin ba kama mutane kawai ba ne.
Muhuyi da kansa ya bayyana cewa manufar kwamitin ta haɗa da daƙile hanyoyin shigar miyagun ƙwayoyi, gyara waɗanda suka faɗa cikin matsalar ta hanyar horaswa da gyaran hali, da kuma gurfanar da masu safarar miyagun ƙwayoyi a gaban kotu.
Don haka, duk wanda yake kallon samamen a matsayin “kama matasa kawai”, ya yi gaggawar yanke hukunci.
Amma ga wani abu mafi tayar da hankali da Muhuyi ya bayyana.
Ya ce daga cikin mutanen da aka kama akwai waɗanda suke iƙirarin sun kashe mutane fiye da biyar, amma ba a taɓa ɗaukar wani mataki a kansu ba. Wato suna yawo a cikin al’umma kamar mutanen da suka fi ƙarfin doka. Wasu kuma, da zarar an kama su, iyayensu sukan zo suna roƙon a sake su, alhali matsalar ta samo asali ne daga rashin tarbiyya da rashin kulawar da ya kamata daga gida.
Wannan magana ya kamata ta girgiza duk wani uba da uwa.
Domin idan ɗanka ya shiga shaye-shaye, ya fara ɗaukar wuƙa, ya fara shiga ƙungiyoyin ’yan daba, ya fara tsoratar da makwabta, sannan duk lokacin da aka kama shi ka fara neman wanda za ka kira domin a sake shi, to me kake koya masa?
Kana koya masa cewa doka ba ta da ƙarfi a kansa. Kana koya masa cewa duk laifin da zai aikata, akwai wanda zai fito ya kare shi. Kana taimaka masa ne, ko kuwa kana shirya masa makoma mafi muni?
A wasu lokuta iyaye suna ganin kare ɗansu daga jami’an tsaro shi ne soyayya. Amma akwai lokacin da soyayya ta gaske ita ce ka bari ɗanka ya fuskanci sakamakon abin da ya aikata domin ya gyara rayuwarsa.
Ba za ka taimaki ɗanka ba idan duk lokacin da ya yi laifi ka yi amfani da sunan iyaye wajen cire shi daga hannun doka.
Ka taimake shi ne idan ka kai shi neman magani idan ya kamu da shaye-shaye. Ka taimake shi idan ka tilasta masa ya koyi sana’a. Ka taimake shi idan ka sa ido kan abokansa da inda yake zuwa. Ka taimake shi idan ka koya masa cewa rayuwar mutum tana da daraja.
A nan ne kuma ya kamata mu kalli abin da Gwamnatin Tarayya ke yi.
Wannan ba matsalar Kano kaɗai ba ce. Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi da shaye-shaye cikin muhimman abubuwan tsaro da lafiyar al’umma. Shugaban ƙasa ya sake naɗa Brigadiya Janar Mohammed Buba Marwa a matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) na wa’adin shekaru biyar, yana mai cewa yaƙin miyagun ƙwayoyi ba yaƙin masu safara kaɗai ba ne, amma yaƙi ne da wata barazana da ke lalata musamman matasa.
ƙididdigar NDLEA ta nuna girman matsalar.
A cikin shekaru biyar da suka gabata, hukumar ta ce ta kama mutane 77,792 da ake zargi da laifukan miyagun ƙwayoyi, ciki har da manyan dillalai 128; ta kwace sama da kilogram miliyan 14.8 na miyagun ƙwayoyi, sannan ta samu hukuncin kotu kan mutane 14,225. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne, hukumar ta kuma ce mutane 32,442 da suka kamu da shaye-shaye sun samu tallafin ƙwararru ta hanyar ba su shawara, magani da gyaran hali.
Wannan shi ne abin da ya kamata mu fahimta: yaƙi da shaye-shaye ba yaƙi da masu shaye-shaye kawai ba ne; yaƙi ne da masu samarwa, masu safara, masu rarrabawa, da kuma tsarin da ke ba miyagun ƙwayoyi damar shiga hannun matasa.
A ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, NDLEA ta ce a cikin shekaru biyu da rabi ta kama mutane 45,853, ta kwace sama da kilogram miliyan 8.5 na miyagun ƙwayoyi, ta samu hukuncin kotu kan mutane 9,263, sannan ta taimaka wajen ba mutane 26,613 masu fama da shaye-shaye shawara da gyaran hali.
A Kano ma, matsalar ba ƙarama ba ce. NDLEA ta ce a shekarar 2025 kaɗai ta kama mutane 1,389 tare da ƙwace sama da kilogram 7,773 na miyagun ƙwayoyi iri-iri. A shekarar 2024 kuma, rundunar ta ce ta kama mutane 1,345 tare da ƙwace sama da kilogram 8,430 na miyagun ƙwayoyi, sannan ta samu hukuncin kotu kan mutane 128.
To, idan waɗannan alƙaluma ba su sa mu firgici ba, me zai sa mu firgita?
A Kano, an samu samamen da suka kai ga kama mutane 28 tare da wargaza wuraren shaye-shaye guda biyar a Rimin Gado da Doka. Muhuyi ya ce fara aikin a garinsu ba don nuna isa ba ne, sai dai domin nuna cewa babu al’umma da za ta kasance sama da doka.
Don haka, idan wani ya ce aikin Muhuyi ya yi tsauri, ina so ya yi tunani kafin ya yi magana.
Shin ya taɓa ganin mutum an sare shi da wuƙa Shin an taɓa saran ɗansa, ɗan uwansa, abokinsa ko makwabcinsa? Shin ya taɓa shiga asibiti ya ga matashi da aka daɓa wa wuƙa saboda rikicin da ya samo asali daga ƙungiyoyin ’yan daba?
Idan bai taɓa fuskantar hakan ba, wataƙila shi ya sa yake ganin samamen jami’an tsaro a matsayin wuce gona da iri.
Amma wanda ya taɓa karɓar kiran waya da aka ce masa, “An soki ɗanka da wuƙa”, ba zai yi saurin raina wannan yaƙi ba.
Wanda ya taɓa zuwa asibiti ya ga jini yana zuba daga jikin ɗansa, ba zai ce a bar masu ɗaukar makamai saboda “haƙƙin ɗan Adam” kawai ba.
Kuma wanda ya taɓa rasa ɗan uwansa saboda rikicin ’yan daba, ba zai yi wasa da kalmar “shaye-shaye” ba.
Haƙƙin ɗan Adam yana da muhimmanci. Amma ina haƙƙin mutumin da aka soka da wuƙa? Ina ne haƙƙin yaron da ya rasa mahaifinsa saboda tashin hankali? Ina ne haƙƙin iyalin da ɗansu ya dawo gida a cikin makara?
Haƙƙin ɗan Adam ba ya nufin ’yancin cutar da wasu.
Abin da ake buƙata shi ne a haɗa tsauraran matakan doka da cikakken bin ƙa’idojin adalci. A kama wanda ya kamata a kama, a gurfanar da wanda ake da hujjar tuhuma a kansa, a hukunta wanda kotu ta samu da laifi, sannan a ba wanda matsalar shaye-shaye ta kama damar samun magani da gyaran hali.
Wannan shi ne abin da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙarfafawa.
Ya kamata kuma a daina barin nauyin yaƙi da shaye-shaye a wuyan jami’an tsaro kaɗai.
Makaranta tana da rawa. Iyaye suna da rawa. Malamai suna da rawa. Sarakuna suna da rawa. Malaman addini suna da rawa. ’Yan jarida suna da rawa. ’Yan siyasa suna da rawa. Al’umma baki ɗaya tana da rawa.
Kuma musamman ’yan siyasa su daina amfani da matasan da suka kamu da shaye-shaye wajen tayar da hankali, zuga su zuwa tashin hankali ko amfani da su a matsayin ’yan daba.
Idan muka yi shiru a yau, kada mu yi mamaki idan gobe wuƙa ta dawo ƙofar gidanmu.
Domin shaye-shaye ba ya tambayar wanda zai cuta. Daba ba ya tambayar wanda zai soka. Laifi ba ya tambayar gidan da zai shiga.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190.
