Tazara yayin haihuwa da muhimmancinta 

Spread the love

Daga DR. BILKISU YUSUF ALI

Haihuwa gaba-gaɗi ba tare da tsari ba na nufin yawan samun juna biyu da haihuwa cikin ɗan gajeren lokaci ba tare da ba wa uwa isasshen lokacin farfaɗowa ba ko yin shiri bisa ƙarfin iyali. Wannan takarda ta yi nazari kan tasirin hakan ga lafiyar uwa da jariri, tarbiyyar yara, walwalar iyali da tattalin arzikin ƙasa.

Bincike ya nuna cewa tazarar haihuwa mai kyau, tare da samun ingantattun ayyukan kula da lafiyar uwa da yaro da ilimantar da iyaye, na taimakawa rage mace-macen mata da jarirai, inganta tarbiyya da kuma bunƙasa tattalin arziki. Iyali shi ne tubalin al’umma. Lafiyar uwa, lafiyar jariri da ingantacciyar tarbiyya suna da muhimmanci wajen gina ƙasa mai cigaba. Saboda haka, tazarar haihuwa cikin hikima da tazarar da ta dace yana taimakawa wajen kare lafiyar uwa da yaro da kuma inganta rayuwar iyali.

Haihuwa a kai a kai  cikin ɗan gajeren lokaci na iya ƙara haɗarin wasu matsalolin lafiya ga uwa da jariri, musamman idan uwa ba ta samu lokacin murmurewa ba.

Ma’anar Haihuwa gaba-gadi ba tare da tazara ba

Ana nufin samun juna biyu da haihuwa cikin ɗan gajeren lokaci ba tare da yin la’akari da lafiyar uwa, ƙarfin tattalin arzikin iyali ba  ko damar kula da yara yadda ya kamata ba.

Masana lafiya suna ba da shawarar a ba jiki lokaci ya farfaɗo bayan haihuwa kafin sake samun ciki, domin hakan yana rage haɗarin matsalolin lafiya ga uwa da jariri.

Illolin haihuwa ba tare da tazara ba , akwai gajiyar jiki.

Haihuwa da ke biyo juna na iya hana jikin mace samun isasshen lokacin murmurewa.

ƙarancin Jini (Anemia).

Mace na iya fuskantar ƙarancin jini saboda yawan haihuwa da rashin samun lokacin dawo da sinadaran da jiki ya rasa.

ƙarin haɗarin matsalolin ciki da haihuwa. 

A wasu lokuta, tazara mai gajarta tsakanin haihuwa na iya ƙara haɗarin wasu matsaloli yayin ciki ko haihuwa.

Matsalolin lafiyar tunani da gajiya da  damuwa da nauyin kula da yara da yawa na iya shafar walwalar tunanin uwa.

Tasirin tazara ga lafiyar jarirai

ƙarin haɗarin haihuwa kafin lokaci.

Ƙarin yiwuwar ƙarancin nauyin haihuwa.

Wahalar samun kulawa idan iyali na da yara da yawa cikin lokaci kaɗan.

Matsalolin gina jiki idan albarkatun iyali sun yi ƙasa.

Illolinta ga tarbiyyar yara

Rashin isasshen kulawa

Iyaye na iya samun wahalar ba wa kowane yaro kulawar da yake buƙata.

Tasiri Kan Ilimi

ƙuntataccen hali na kuɗi na iya shafar damar yara zuwa makaranta ko samun kayan karatu.

Tasiri kan tarbiyya

Idan iyaye sun yi nauyin kula da yara da yawa lokaci guda, hakan na iya rage lokacin da suke ba wa tarbiyya da sa ido.

Illolinta ga iyali

Ƙarin nauyin rayuwa.

ƙara matsin tattalin arziki.

Damuwa tsakanin ma’aurata.

Rage damar tara dukiya da zuba jari.

Illolinta ga tattalin arziƙin ƙasa

ƙarin nauyi ga ayyukan Lafiya

Ana buƙatar ƙarin kuɗaɗe wajen kula da mata masu juna biyu da jarirai.

ƙarin Buƙatar Ilimi

Yawan yara na ƙara buƙatar makarantu, malamai da kayan aiki.

Matsin lamba kan ababen more rayuwa

Yawan jama’a na iya ƙara matsin lamba kan gidaje, ruwa, lantarki da sauran ayyukan gwamnati.

Rage tanadin Iyali

Iyali na iya kashe mafi yawan kuɗinsu wajen kula da buƙatun yau da kullum maimakon saka hannun jari.

Fa’idodin tsara iyali da tazarar haihuwa

Kare lafiyar uwa.

Inganta lafiyar jarirai.

Sauƙaƙa tarbiyya.

Ba iyali damar tsara kuɗinsu.

ƙarfafa damar yara samun ilimi da kulawa.

Rage mace-macen mata da jarirai.

Hanyoyin Magance Matsalar

Ta ɓangaren iyaye

Su tattauna kan tsara rayuwar iyali.

Su nemi shawarwarin ma’aikatan lafiya.

Su kula da lafiyar uwa kafin da bayan haihuwa.

Taimakon  ma’aikatan lafiya

Su wayar da kai kan muhimmancin tazarar haihuwa.

Su ba da shawarwari bisa ilimin likitanci.

Rawar da gwamnati za ta taka

Ta ƙara inganta cibiyoyin kula da lafiyar uwa da yaro.

Ta tallafa wa shirye-shiryen wayar da kai.

Ta inganta ilimin mata da yara.

Shawara ga shugabannin addini da al’umma

Su ƙarfafa kula da lafiyar iyali.

Su wayar da kai game da muhimmancin uwa da yaro su kasance cikin ƙoshin lafiya.

Shawarwari

A ƙara ilimantar da ma’aurata game da muhimmancin tazarar haihuwa.

A ƙarfafa mata su halarci kula da ciki da bayan haihuwa.

A bunƙasa ilimin mata da ‘yan mata.

A inganta tattalin arzikin iyalai.

A ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, ma’aikatan lafiya, malamai da shugabannin addini wajen wayar da kai.

Kammalawa:

Haihuwa gaba-gaɗi ba tare da tsari ba na iya haifar da ƙalubale ga lafiyar uwa da jariri, tarbiyyar yara, walwalar iyali da tattalin arzikin ƙasa. Yin shiri cikin hikima, ba da muhimmanci ga lafiyar uwa, da neman shawarwari daga ƙwararrun ma’aikatan lafiya na taimakawa wajen gina iyalai masu ƙoshin lafiya da al’umma mai ɗorewa. Manufar ita ce a tabbatar cewa kowace uwa da kowane yaro suna samun kulawar da ta dace da kuma damar rayuwa cikin koshin lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply