Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Zallawa sun rasa yadda za su ɓoye muguwar manufarsu ta Biyafara da neman ware Arewa ta tsakiya daga Arewa da sunan midil bel, sun fara ganin uwar bari sun nuna alamun mika wuya. Kazalika su ma wadanda ke shigar burtu da sunan ƙarya na Musulmi na wahala wajen shigar burtu
Akwai alamun matsin lamba daga AIFOB ga Zallawa su fito fili kawai su tallata muradin kafa Biyafara. Wanda ya ci ladan kuturu ai dole ya yi ma sa aski. Tun su na nuna gwamnatin marigayi Buhari ta zalunci madugunsu Nnamdi Kanu har ta kai ga ba abun da za su iya fakewa da shi yayin da Jostis James Omotosho na babbar kotun tarayya ya yanke ma sa hukuncin ɗaurin rai da rai. Yanzu sun shiga nuna goyon baya ƙarara na kafa Biyafara da hakan ya tabbatar da su Midibelawa ne da dama sun ɗauka ko ‘yan Biyafara ’yan uwansu ne. Ka san Zallawa wayo gare su amma ba hankali. A shekarun baya akwai wasu sassa na jihar Kaduna da ma wasu al’ummar jihar Binuwe da ke nuna goyon baya ga Biyafara da nuna matuƙar Nijeriya ta rabu to su ɓangaren Biyafara za su marawa baya kuma can za su haɗe da ’yan awaren. Su na maganar cikin alfahari da karsashi.
Duk wani ɗan AIFOB ko dan barandar AIFOB a Zallawa da ke bagaye da sunan Musulmi za ka ga ba hoto ba sunan gaskiya ko shafinsa a rufe ya ke ruff LOCKED PROFILE. Wallahi akwai katti GARDAWA da ke nuna su mata ne don hakan ya ba su damar wurga baƙaƙen maganganu da yayata sharri. In ba tsoro ba su fito fili ma na. Ai duk mai irin waɗannan manya-mayan miyagun maganganu ba zai lauye da cewa wai ya na gudun kar a hallaka shi ne ya ke buya alhali shi da masu hallakawar Danjuma ne da Danjummai THE BANZALES.
Duk mugu da ke shigar burtu wai shi Bahaushe ne alhali Bakadamushe ne zai nuna wai don Hausawa sun ce za su kafa ƙungiya shi ne a ke zarginsu da kafurci. Yo akwai wata kungiya a Nujeriya ta ko ma waye har ma AIFOB ɗin da membobinta ke ɓoye ruff har ma jibgegen kato ya nuna shi wata ’yar yarinya ce? Kai koma a nemo hoton wata mai kama da Hindiya a AI a ce ai ga wacece-wacece ta Hausa. Haba Kadamusawa yaushe za ku daina yaudarar kanku da sauran ‘yan kasa?.
’Yan AIFOB da wasu tarkace a Midibelawa na fitowa su ingiza wannan fitina duk da a tarihi ba su taɓa ƙaunar Hausawa ba. Kai ko yanzu da dai za su cimma buri, za su fito a mutum don Bahaushe tun da ba zai bar addininsa ba, to ba za su taɓa kaunarsa ba. Rubutu da Hausa ko baƙar magana da Hausa ko kafa ƙungiyar ƙarya da lankaya Hausa ba za su taba maida mutum Bahaushe ba sai dai Bakadamushe don shi KADAMUS ba ya hango nesa fiye da hancinsa.
Zallawa sun shirga karya har sun gajiyar da kan su don arewa ta ƙi kamawa da wutar da su ke ta izawa da zuga-zugi dare da rana. Da wutar ta tashi bau sai a sheƙa rowan sama ko ina ya yi male-male. Sunan shehu Mujaddadi kuma ya gagari bakin fentinsu. Ba irin batanci da ba sa yi wa Mujaddadi da sauran magabata da su ka ba da gudunmawa ta Mahadi ka ture wajen gina Arewar da mu ke cin moriya a zamanin yau. Wasu ma har sadaukar da ransu su ka yi kamar Sir Ahmadu Bello da Sir Abubakar Tafawa Balewa Allah ya jikan su da rahama.
Don yawan shirga karya na Zallawa har wasunsu kan ja hankalin waɗanda su ka fi zarmewa cewa wani abun ba gaskiya ba ne. Akwai wani da ya zuba rubutu don tada fitina ya cusa ƙabilanci a fitinar yankin Bargu, sai wani mai sharhi ya taka ma sa birki da nuna ya yi karin gishiri a labarin. A baya ba a samun irin wannan gyara don mutanen ’yan za ni ne kan tarar da mu je.
A tsakaninsu ma su na jifar juna da makirci kuma hakan na nuna nan gaba kaɗan za su shiga zubawa juna baƙar magana don ƙarfin kwangilar nan zai ragu bayan babban zaɓen 2027 wato nan da wata 4 in Allah ya kai mu. Da alamu hakan ya sa wasu su ka zama dillalan zallallun ’yan siyasa don in sun lashe zaɓe su riƙa samun abun masarufi da shirya tarukan sharri. Duk da haka ba wani dan siyasa ko daya da ya yarda ya nuna kansa tare da wani Bazalle don ‘yan siyasar nan sun san ba mai lashe zabe a doron ƙabilanci ko ta irin makircin Zallawa na zagin Shehu Mujaddadi a nan dai Arewa. Dama da muguwar rawa gwamna kin tashi kuma ina ribar baɗi ba rai kuma yaya mutum zai sayar da randa ya sai kwanda don tara ruwan sha.
Ba wani Bazalle da ya taba gigin ya ɗau hoto da wani shahararren ɗan siyasa balle har ya ce wannan shi ne dan takararsa na Zallawa. Abun takaicin ma shi ne yaushe ‘yan AIFOB su ka mallaki hankalin da za su ke jan akalar Zallawa da tsara mu su manufofi? Kawai in AIFOB na da maƙudan kuɗi na makirci ta cigaba da kashewa amma tabbas ‘yan AIFOB ba su gwanance wajen magana ba. Hasalima su kan yi sanadiyyar tonawa ‘yan barandarsu asiri ne. Da son samu ne su riƙa aiki ta ƙarƙashin ƙasa amma fitowar nan da su ke yi ita za ta sa watakil har Mahadi burinsu na Biyafara ba zai cimmu ba.
Gaskiyar magana masu tsarawa Zallawa manufofi ko hanyoyin kulle-kulle ba su gane yadda Arewa ta ginu da ƙarfi kan lamuran Musulunci ba ne don sun dauka in sun dinkawa munafukai rigar Hausawa da sunan wai a na zaluntar Hausawa shikenan sai wuta bal-bal-bal daga nan su nufi Enugu ko Anacha don taron kafa ƙasar aware! Su kuma tarkace na cewa wai ayyukan nan na Musulunci da Shehu Mujaddadi ya shimfiɗa su ne ɓarayin daji ke kammalawa! to da ɓarayin su ka rubuta littafi ko su ka yi sallah ko azumi ko fitar da zakkah? Haba ga gaskiya nan sai wasu matsorata masu ɓuya ruff a soshiyal midiya ba su ma ko iya karatun Baibul ba wai su ne za su faɗawa mai sallah sau 5 a wuni yadda zai gudanar da rayuwarsa! Allah ya tsari gatari da saran shuka.
Ba kawai yayata labaran marar sa inganci ne illar waɗannan mutane masu shigar burtu ba, yanzu sun fara nuna niyyar amsa kiran AIFOB na fitowa don yin zanga-zanga. Kar gigin soshiyal midiya ya sa Zallawa kirarin yin zanga-zanga a Arewa don da alamu mutanen nan sun yi miƙa su na neman wuce bargonsu
Tun kwanaki na ga wasu ‘yan AIFOB na ingiza Zallawa wai su yi gangami don kawar da sarakunan Arewa su naɗa Zallawa. Ina ganin a watan gobe wannan wa’adi na zuga zai cika. Ba mamaki na ga wasu na yayata wai Zallawa sun yi zanga-zanga a can kudu da sunan matsa lamba ga gwamnati wai ta dakatar da farmakin kare dangi kan Hausawa. Akwai wata takardar sanarwar da masu wannan tunzuri su ka yayata na yin taro na Allen Avenue da ke anguwar Ikeja a Legas. Hotunan bidiyo sun nuna wannan taro ya juye ya koma zanga-zanga duk da mutanen kalilan ne kuma wai su na maganar neman ‘yancin Hausawa? Waɗanne Hausawan ne ba su da ’yanci? Wannan shi ke nuna tsananin makirci na maƙiya Arewa.
Duk masu hankali sun san wannan makirci ne kawai don ƙalubalen tsaron Arewa ba ya ware Musulmi ba ya ware Kirista, hakanan ba abun da ya haɗa wannan da ƙabilanci ko wata ƙabila.
Hatta wani hoto da na gani wasu ‘yan tsiraru sun daga kwali abun takaici wai a ce su ne za su yi shigar burtu a matsayin wai Hausawa ne. Akasari sun sa riguna digil-digil kuma wanda ya shiga gaba a wani hoto ma tamkar irin magoya bayan ƙungiyar kwallon kafa ne ya yi wani zabura haka. Ina manyan Hausawanmu na Legas da sauran jihohin kudu maso yammacin Nijeriya? Kai wannan farafaganda ce kawai don ko hayar mutum 10-15 za a ɗauka a miƙa mu su kwalaye a ɗau hotuna a wurgo a soshiyal midiya. Ahir wannan zolaya kar a shigo da ita Arewa. Zaman lafiya mu ke nema. Kuma na tabbata hukumomi na zuba ido ga mai kunnen kashi.
KAMMALAWA
Al’ummar jihohin da ƙalubalen ya yi ƙamari irin Katsina, Zamfara, Sokoto, Kaduna da Neja duk sun fito sun barranta fitinar da ƙabilanci. Mai ya sa wasu ‘yan barandar AIFOB za su ke hura wuta wai lallai sai sun maida wannan ƙalubale ya zama ƙabilanci? Su dai tsaya a yanar gizo kar su yi gigin gwada irin wannan shaidancin a titunan Arewa.
Duk wanda ya zabi zama lafiya ya yi kansa ƙiyamul laili amma wanda ya ga tsayuwar wata ba ta burge shi ba sai ya gwada hawa ko ya gyara. Masu kishin Arewa na nan kullum wajen samu hanyoyin maslaha da za su samar daf akin zaren magance ƙalubalen tsaro kuma ko yanzu an fara samun sauki. Mu na ƙara godewa Allah.
