Ƙuri’a ɗaya ta kawo ƙarshen mulkin Netanyahu na shekara 12 a Isra’ila

Daga AMINA YUSUF ALI

Firayiminista Benjamin Netanyahu, kuma firayiminista mafi daɗewa a Ƙasar Isra’ila ya yi adabo da kujerarsa. Hakan ta faru ne bayan majalisa ta sutale shi tare kuma da maye gurbinsa da wani sabon Firayiministan wanda aka zaɓo shi ta hanyar haɗin gwiwa da jam’iyyun siyasar da suke a ƙasar.

A halin yanzu tuni sabon Firayiminista Mista Bennet ya ɗare kujerar Netanyahu wanda ya shafe tsawon shekaru goma sha biyu a matsayin firayiminista a ƙasar.

Mr. Bennet dai ɗan ɓangaren mulkin ra’ayin riƙau ne na ‘yan ƙasa. Kuma ana sa ran zai shafe shekaru biyu yana riƙe da matsayin kafin daga bisani ya miƙa kujerar ga ɗan ɓangaren tsaka-tsaki, Yesh Atid kamar yadda suka ƙulla yarjejeniyar kama-kama tsakanin ɓangarori na ƙasar.

Netanyahu dai ya rasa kujerarsa ne bayan majalisa ta tafka muhawara sannan aka yi zaɓen cancantarsa da rashinta ci gaba da zama kan kujerar. Inda ya samu ƙuri’u 59 cikin sittin. Wato ya kasa da ƙuri’a guda ɗaya tal. Wacce ta tilasta masa ya sauka daga kujerarsa ta firayiminista.

Jim kaɗan bayan kammala muhawarar, Netanyahu bai yi ƙasa a gwiwa ba. Ya miƙe zuwa inda sabon firayiminista Bennet yake. Inda ya miƙa masa hannu ya taya shi murna. Inda ya ƙare maganarsa da gargaɗi ga Bennet: “ina nan zan sake dawowa kan kujerata”.

Bisa dukkan alamu wannan naɗi da aka yi bai yi wa wakilan Falasɗinawa ba. Domin sun nuna rashin girmamawa ga zaɓin majalisar.

Shi ma a nasa ɓangaren, Shugaba Biden na ƙasar Amurka ya aiko da saƙon taya murna ga Bennet. Inda ya ƙara da cewa, yana mai ɗokin ganin sun yi aiki tare.