Boko Haram na yaudarar mayaƙansu da Naira 5,000 – Zulum

Daga WAKILINMU

Gwamnan Jihar Barno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram suna amfani da kuɗi suna yaudarar mutane su shigo cikinsu inda sukan raba musu dubu biyar-biyar (N5,000).

Kazalika, Zulum ya bayyana yadda gwamnatinsa ta sha gwagwarmaya da yaƙi da Boko Haram a tsakanin shekaru biyun da suka gabata.

Gwamnan ya yi waɗannan bayanan ne yayin da yake yi wa talakawansa bayani ta kafar yaɗa labarai game da sha’anin mulkinsa a yayin bikin Ranar Dimukuraɗiyya na bana da aka gudanar a Asabar da ta gabata.

Kazalika, bayanin gwamnan ya shafi bikin cikarsa shekara biyu kan mulkin jihar Barno.

Da yake jawabi, Zulum ya ce baki ɗayan jihohi 36 da Nijeriya ke da su babu jihar da ke fuskantar ƙalubalen tasro da walwalar rayuwa da tattalin arziki  kamar Barno.

Ya ce daga ranar da ya soma mulkin jihar Barno ya fahimci irin jinƙan da jihar ke buƙata, musamman ma yankin arewacin jihar da wasu sassa daga mazaɓun sanata na tsakiya, kan haka ne ya ce ya duƙufa aiwatar da ayyukan jinƙai da kyautata rayuwar ‘yan jiharsa.

Gwamnan ya zayyano tarin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannoni daban-daban tun kafuwarta, tare da bai wa talakawansa  tabbacin ci gaba da yi musu hidima gwargwadon hali.