Gona zan koma bayan na yi murabus daga siyasa – Masari

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya ce zai yi murabus daga harkokin siyasa bayan kammala wa’adinsa  a matsayin gwamna.

Masari ya bayyana haka ne sa’ilin da yake yi wa taron maneman labarai bayani a Katsina yayin bikin Ranar Dimukuraɗiyya na bana da ya gudana ran Asabar da ta gabata.

Gwamnan ya ce bayan kammala mulkinsa zai yi murabus daga siyasa sannan ya koma gonarsa ya ci gaba da noma.

A cewarsa, “Na riƙe muƙamai da dama kama daga matsayin kwamishina a jihar Katsina zuwa Majalisar Ƙasa inda na riƙe matsayin Shugaban Majalisar Wakilai.

“Ga shi har yanzu ina yi wa jama’ata hidima a matsayin Gwamnan Jihar Katsina. Me kuma nake buƙata?

“Mutanena daga Katsina, kamar marigayi  Umaru Musa Yar’adua ya yi takarar shugaban ƙasa kuma ya ci, haka ma Muhammadu Buhari wanda ya yi shugaban ƙasa a mulkin soja.”

Ya ci gaba da cewa, “Ina ganin lokaci ya yi da za mu bai wa wasu fage su ma su taka rawarsu sannan mu koma wani ɓangare.

Masari ya ce babban al’amrin da ke gabansa yanzu shi ne, yadda zai gyara duka abubuwan more rayuwa da suka lalace a faɗin jihar domin dawo da martabar jihar kamar yadda aka san ta a can baya.

“Bayan na cika wannan ƙuduri, zan yi murabus in koma gonata,” in ji gwamnan.