Gwamnati ta dakatar da albashin ma’aikata 331 saboda rashin cika umarnin IPPIS

Daga WAKILINMU


Gwamnantin Tarayya ta ce ta dakatar da albashin wasu ma’aikata su 331 saboda rashin ba da cikakken bayanansu a tsarin biyan albashi na IPPIS kamar yadda aka buƙaci kowane ma’aikaci da aikatawa.

Babban Sakatare na Ofishin Gudanar da Ayyuka, Mahmuda Mamman, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ta hannu Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya, Abdulganiyu Aminu, a ranar Asabar da ta gabata a Abuja.

Kamar yadda sanarwar ta nuna, Mamman ya sanya wa takardar sanarwar hannu a madadin Shugaban Ma’aikata, Dr. Folasade Yemi-Esan.

Kazalika, sanarwa ta ce an tura takarda zuwa ga ɗaukacin manyan sakatarori da Akanta Janar na Ƙasa haɗa da Babban Jami’in Bincike na Ƙasa.

Mamman ya ce An dakatar da albashin ma’aikatan su 331 a tsarin IPPIS saboda rashin bada cikakken bayanansu ta intanet kamar yadda aka buƙace su da yi.

Haka nan, ya ce duk da irin yayatawar da aka yi kan kowane ma’aikaci ya tabbatar ya shiga intanet ya ba da cikakken bayanansa a shafin tantance ma’aikata ƙarƙashin IPPIS, amma duk da haka wasu ma’aikatan sun ƙi cika wannan umarni.

Wannan ne kuma ya sa ma’aikatan da lamarin ya shafa suka kasa shiga shirin tantance ma’aikata na zahiri da aka gudanar tsakanin Yunin 2018 da Disamban December 2020 sakamakon rashin samun bayanansu.

Da wannan ne Mamman ya ce ana buƙatar ma’aikatan da lamarin ya shafa da su je ofishin Darakta (IPPIS-SW) a Ofishin Shugaban Ma’aikata don ƙarin bayani da kuma tantance su.

Gwamnati ta samar da tsarin biyan albashi na IPPIS ne don kawar da matsalar ma’aikatan bogi da kuma taƙaita wa kanta kashe kuɗaɗe don samun sauƙin gudanarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *