Daga BASHIR ISAH
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi ganawar sirri tare da gwamnonin APC ranar Talata a Fadarsa da ke Abuja domin tattauna batun wanda zai zame wa Tinubu mataimaki a babban zaɓen 2023.
Gwamnonin sun iyarci Buharin ne ƙarƙashin ƙungiyarsu ta Progressive Governors’ Forum (PGF), ƙarƙashin jagorancin Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.
Bayanan da Manhaja ta kalato sun ce, mahalarta taron sun haɗa da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, Gwamna Babagana Zulum na Borno, Nasir El-Rufai na Kaduna, Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa, Abdullahi Sule na Nasarawa, Simon Lalong an Filato, Yahaya Bello na Kogi da kuma Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo.
Bayanai sun nuna Bola Tinubu ya zaɓi tsohon Gwamnan Borno, Ibrahim Shettima ne a matsayin wanda zai yi masa mataimaki saboda rawar da ya taka wajen yakin neman zabensa.
Sai dai, majiyarmu ta wasu ‘yan Jam’iyyar CPC, jam’iyyar da ta ba da gudunmawa wajen kafa APC, na shirin ganawa da Shugaba Buhari domin ba da shawara kan ko a zabi Babban Lauyan Ƙasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ko kuma Ministan Sufurin Jirgaen Sama, Hadi Sirika a matsayin mataimakin Tinubu.
Haka nan, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babagana Kingibe, wanda ya yi wa marigayi MKO Abiola mataimaki a zaben Yunin 1993, ya mika wa Gwamnan Atiku na Jihar Kebbi, wasu sunaye guda uku don ya miƙa wa Tinubun ya zaɓi mutum guda daga ciki da su yi takara tare.
Sunayen da Kingibe ya miƙa ɗin su ne na; Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum da Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina J. Mohammed da kuma tsojon jami’in hulda na Majalisar Tarayya a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, Kashim Ibrahim-Imam.
Sai dai duka waɗanda lamarin ya shafa baki ɗayansu Musulmai ne daga shiyyar Arewa maso Gabas. Kuma miƙa sunayen ya biyo bayan ƙorafin da aka yi ne kan cewa APC na shirin tsayar da Musulmai a matsayin ‘yan takararta.
Lamarin da aka ce bai yi wa Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya da kuma wasu masu ruwa-da-tsaki na APC daɗi ba.