An tsaurara matakan tsaro yayin rantsar da zaɓaɓɓun Ciyamomi da kansiloli a Abuja

Daga AMINA YUSUF ALI

An tsaurara matakan tsaro ainun a garin Abuja a yayin da sabbin zaɓaɓɓun Ciyamomi da Kansiloli suke amsar rantsuwar kama aiki.

Ministan Birnin Tarayyar Abuja, Muhammad Musa Bello shi ne ya jagoranci taron ƙaddamar da rantsuwar sababbin shugabannin ƙananan hukumomi da Kansiloli na gundumoni shida da suke garin Abuja.

Wannan taro da aka daɗe ana dako ya faru ne a cibiyar fasaha da al’adu ta Cyprian Ekwensi wacce take a unguwar Area 10, Garki a garin Abuja. An tsaurara matakan tsaro sosai a yayin gudanar da taron.

Wakilin jaridar Blueprint ya samu yin tozali da zaɓaɓɓen Ciyaman na ƙaramar hukumar ƙwaryar birnin Abuja (AMAC), Mista Christopher Zakka (Maikalangu) a yayin da yake musayar gaisuwa da wasu manyan baƙi da suka halarci taron.

Taron ya samu halartar manyan baƙi da dama. Daga ƙofar shiga wajen taron, an sanya jami’an tsaro da dama domin tantance manyan baƙi, ‘yan jaridu har ma da masu sha’awar shiga wajen taron kafin su shiga ɗin.

Wakilin Blueprint ya bayyana cewa, tun daga bakin ƙofar shiga wajen taron ake umartar wasu magoya bayan jam’iyyu, da waɗanda ba su da alaƙa da taron da su juya su bar wajen taron.

Hakazalika, ‘yan jaridu da dama an hana su shiga wajen taron domin rashin sashihiyar shaidar da za su bayyana kansu da ita. Wasu kuma sai da suka yi kiran wasu abokansa daga ciki domin su sa baki a bar su su shiga.

Yankunan da zaɓaɓɓun Ciyanomi da Kansilolin suka fito su ne, AMAC, Bwari, Kuje, Gwagwalada, Abaji da kuma Kwali.