Daga MALAM ALEE AL-AMIN
Ba za ka san san ruwa ba sa’an kwando ba ne sai ka shiga ka soma ninƙaya a tekun siyasar nan mai matuƙar haɗarin. Domin idan akwai abinda ya fi jarumta kana buƙatarsa kafin ka afka cikin tekun siyasa.
Filin daga ne da da fari ake zaton na masu ƙwanji ne zalla, sai dai tafiyar na yin nisa mata suka fara tsagawa suna kutsawa ciki. Kusan ma yanzu za a ce duk zagayowar kakar siyasa kan zo da hauhawar ƙaruwar mata masu buƙatar dafa madafun iko, kuma abin sha’awar shi ne, a wannan guguwar sauyin ba a bar matan Arewa a baya ba.
Ƙurewar kololuwar jan hankali shi ne, yadda mata matasa masu jini a jika da ɓargo a kwanya suka ƙi bari a cigaba da tsallake su a siyasar kama madafun iko tun daga matakin jaha har zuwa ga kankat, wato gwamnatin tarayya.
Kuma fa ba wai suna tafe suna kamun ƙafar idan an ci yaqi a ba su kuturun bawa ba ne ta hanyar rabon madafun Alakoro, a’a su ma sun zavi su fito fagen daga ne a yi yaƙin! Su ma su ɗauki tasu ganimar ta iya kuɗinka, iya shagalinka.
Sannan ba su zo hannu rabbana ba domin cike suke da salo da dabarun da lallai idan aka ba su igiyar, za su iya riketa gam gam.
Alal misali, samun mace a karon farko da ta ɗare kujerar mataimakiyar Gwamna a jahar Kaduna, kuma ta yi duk abinda za ta yi na ganin ba ta bai wa mata da al’ummar jahar kunya ba, ya zare lakar tsoro daga zukatan matan. Inda suka fito gadan-gadan da tabbacin su ma fa za su iya.
Hakazalika, Majida Muhammad Sani ‘yar takarar kujerar Majalisar jaha abar buga misali ce ga abinda nake ta haƙilon faɗi a rubutun nan. Domin baya ga tarin dabaru da ƙwarewa da mafarkin da take da shi na yi wa mazaɓarta da jaharta hidima, wannan ‘yar tahalika ta tabbatar wa da masana harkar cewa, ita fa ba kanwar lasa ba ce wajen iya aiwatar da ayyukan da ta yi ƙudirin yi.
Ire-iren Majidar da suka lashi takobin canja salon siyasar dake barinsu a baya sun fara fin a ƙirga a wannan yanki yanzu haka.
Malam Alee Ameen
