2023: Tambuwal ya bi sahun masu kwaɗayin mulkin Nijeriya

Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya fito fili ya bayyana ƙudiransa na neman takarar shugabancin Nijeriya ya zuwa 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki na PDP a jiharsa wanda ya gudana a jiya Litinin.

Gwamnan ya ce, ya yanke shawarar takarar shugabancin ƙasa ne duba da irin nasarorin da ya samu a tarihin siyasarsa.

A cewarsa, “A lokacin da ‘yan Majalisar Wakilai zubi na bakwai suka buƙace ni da in nemi kujerar Shugaban Majalisa na gindaya musu sharuɗɗa.

“Cewa a matsayina na ɗan Sakkwato mai biyayya, sai sun je sun tuntuɓi shugabannina a jiha tukuna kafin in amince da buƙatarsu, hakan kuwa aka yi wanda a ƙarshe muka samu nasara.

“Yau ga mu, na kuma saurari shugabanni da mata da matasa da kuma sauran mambobin PDP a jihar Sakkwato a kan buƙatar in soma tuntuɓa game da takarar shugaban ƙasa.

“Wannan shi ne dalilin da ya sa zan fito in zama ɗan takarar shugaban ƙasa na farko a PDP, ta yadda idan Allah Ya dafa wa gwagwarmayarmu sai in zamo Shugaban Ƙasa na Tarayyar Nijeriya.

“Don haka, da sunan Allah Maɗaukaki, Mai rahma, Mai jinƙai, na amince da in soma shirye-shiryen takarar Shugaban Ƙasar Tarayyar Nijeriya.”

Tun farko, sai da mataimakin gwamnan Sakkwato, Alhaji Mukhtari Shagari, ya yi kira ga al’ummar jihar da su zamo masu godiyar Allah a kowane lokaci da ya ba su shugabanni nagartattu.