Daga BASHIR ISAH
Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda kuma shugaban sashen binciken manyan laifuka na Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa (FCID), Joseph Egbunike ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda jaridar SaharaReporters ta ruwaito.
Bayanai sun nuna Egbunike ya yanke jiki ne ya faɗi a cikin ofishinsa da ke Abuja a jiya Talata wanda daga nan kuma rai ya yi halinsa.
Kafin mutuwarsa, Egbunike shi ne mai kula da sashen bincike mafi girma na rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Aikin sashen da marigayin ya riƙe ya haɗa da binciken manyan laifuffuka da gurfanar da masu aikata mayan laifuka a ciki da wajen ƙasa.
Marigayin shi ne wanda ya gurfanar da DCP Abba Kyari a ƙarshen 2021, amma ya ƙi kama shi da kowane laifi duk da Cibiyar Bincike ta Ƙasar Amurka ta nuna Kyari ya aikata laifi.
Shi ne ja-gaban binciken badaƙalar mu’amala da ɗan damfara Hushpuppi da ake yi a kan Abba Kyari.
Marigayi Egbunike ya yi karatu a Jami’ar Nsukka inda ya samu digiri na ɗaya kan hada-hadar kuɗi (BSc in Accounting). Haka nan, yana da digiri a fannin sanin dokoki da digiri na biyu a fannin hulɗar ƙasa da ƙasa, sai kuma digiri na uku a fannin nazarin manyan laifuka (PhD in Criminology).
