Masana kimiyyar Sin sun isa ƙolin tsaunin Qomolangma

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Tawagar masana kimiyya na ƙasar Sin ta “yanayin duniya na shekarar 2022”, ta yi nasarar hawa tsaunin Qomolangma mai tsawon mita 8,848 a yau Laraba, inda kashi na farko na tawagar ta isa ƙolin da misalin karfe 12:22 na rana, yayin da sauran suka cim musu bayan awa guda.

Mambobi 13 na tawagar da suka tashi da safiyar yau ne suka fara haye mita 8,000, inda 5 daga cikinsu suka kafa cibiyar tantance yanayi mai sarrafa kanta mafi tsawo a duniya da misalin ƙarfe 11:11 na safiya, a kan yankin iyakar Sin da Nepal mai tsawon mita 8800.

Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa

By Editor