Labarin likitocin Beijing da suka samar da agajin jinya ga mutanen Afirka

Daga MURTALA ZHANG

Tun shekaru sama da 50 da suka gabata har ya zuwa yanzu Ƙasar Sin take aiwatar da ra’ayin gina al’umma mai kaykkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya, don tabbatar da ƙoshin lafiyar jama’a. A shekara ta 1963, kasar Sin ta tura tawagar ma’aikatan jinya ta farko zuwa nahiyar Afirka. Kawo yanzu, akwai ma’aikatan jinyar ƙasar Sin da dama wadanda aka tura zuwa Afirka don kulawa gami da samar da magani ga mutanen Afirka, inda aka jinjina musu saboda jajircewarsu wajen kare rayukan al’ummar wurin. Har ma ana kiran likitocin ƙasar Sin da suna “mala’ikar ƙasar Sin sanye da kayan likitoci”.

Waiwaye adon tafiya. Tun a shekara ta 1968 ne, hukumar birnin Beijing, fadar mulkin ƙasar Sin, ta fara tura wata tawagar ma’aikatan jinya 36 zuwa ƙasashen waje. Kawo yanzu, cikin shekaru 54, gaba ɗaya hukumar birnin Beijing ta tura irin wadannan tawagogi 53 zuwa ƙasashe da yankuna 11 a duk faɗin duniya. Daga cikin ma’aikatan jinyar 1011, har akwai guda 12 waɗanda suka sadaukar da rayukansu a ƙasashen da suka yi aikin samar da tallafi. A ƙasashen waje, ba kulawa da marasa lafiya kawai ma’aikatan jinyar ƙasar Sin suka yi ba, har ma sun yi ƙoƙarin kafa asibitoci da ɗakunan gwaje-gwaje, tare kuma da horas da ma’aikatan jinyar wurin, al’amarin da ya sa suka kulla zumunci mai zurfi tare da jama’ar wurin.

Maaikatan jinyar ƙasar Sin na samar da agaji don dakile cutar Ebola a ƙasar Guinea

A watan Agustar shekara ta 2021, an kafa tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin karo na 29 da suka je kasar Guinea don samar da tallafi, inda kuma aka ba su horo a fannoni daban-daban, ciki har da yaren Faransanci, da ƙa’idojin harkokin waje da sauransu. Daga cikin ma’aikatan jinyar guda 22, akwai 20 waɗanda suka zo daga asibitin Tiantan dake birnin Beijing. A nasa ɓangare, shugaban asibitin, Wang Yongjun ya bayyana cewa, a lokacin da cutar mashako ta COVID-19 ke ci gaba da addabar duniya, tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin ta tafi Guinea don samar da tallafi, abun da ya sa suka cancanci yabo matuka.

A ranar 6 ga watan Maris din bana, waɗannan ma’aikatan jinyar ƙasar Sin sun isa Conakry, fadar mulki ƙasar Guinea, inda suka fara aikin samar da agajin jinya har na tsawon watanni 18. Shugaban tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin karo na 29 da suka je Guinea, Mista Guo Wei ya ce, ban da samar da agajin jinya, likitocin ƙasar Sin za su faɗaɗa haɗin-gwiwa tare da takwarorinsu na ƙasar, a fannonin da suka shafi kiwon lafiya, kula da harkokin asibiti, gyare-gyare ga likitanci da sauransu. 

Zhang Wei shi ne shugaban tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin karo na 28 da aka tura zuwa Guinea, ya waiwayi ayyukan da tawagarsa ta yi a Guinea, inda ya ce, yaɗuwar cutar COVID-19, gami da wasu cututtuka, ciki har da maleriya. da shawara, da Ebola, da kyanda, duk sun haifar da ƙalubale ga rayuwar jama’ar ƙasar.

Kwararrun likitocin ƙasar Sin na faɗakar da likitocin Guinea kan ilimin kandagarkin cutar COVID-19

Tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin ƙarƙashin shugabancin Zhang Wei, ta yi namijin ƙoƙarin don haɗa kai tare da cibiyoyin kiwon lafiya na Guinea, a fannin musanyar fasahohin aikin jinya, da samar da kayayyaki da horo kyauta, abun da ya taimaka sosai ga dakile yaɗuwar cututtukan COVID-19 da Ebola a ƙasar.

Mista Zhang Wei ya ƙara da cewa, zuwa watan Maris din shekara ta 2022, an kafa kwamitin daƙile cututtuka masu yaduwa a asibitin sada zumunta na Sin da Guinea, da samar da horo ga ma’aikatan asibitin a fannin hana yaɗuwar cututtuka, da ilimin da ya shafi sanya takunkumin baki da hanci da tsabtace wurin aiki da sauransu.

Idan mun dubi tarihin samar da agajin jinya da likitocin birnin Beijing na ƙasar Sin suka yi a ƙasashen ƙetare, tun a ranar 8 ga watan Yunin shekara ta 1968, Wang Huaiqing da sauran wasu kwararrun aikin jinya daga cibiyoyi daban-daban na Beijing, sun yi tattaki zuwa ƙasar Guinea dake yammacin Afirka, inda suka buɗe babin samar da agajin jinya da ma’aikatan Beijing suka yi.

Ƙasar Sin ta samar da agajin allurar rigakafin cutar COVID-19 ga Guinea

Daga bisani, akwai likitocin Beijing masu tarin yawa, waɗanda suka bayar da hidimomin jinya ga ƙasashe daban-daban, ta hanyoyin bada magani, da kula da marasa lafiya, da dakile yaɗuwar cututtuka, da samar da kyautar kayan aikin likita da faɗakar da al’umma kan likitancin gargajiyar ƙasar Sin da sauransu. Har wa yau, likitocin Beijing sun horas da dimbin ma’aikatan jinyar ƙasashen waje, musamman na Afirka, don inganta kwarewarsu a fannin aikin jinya.

A shekara ta 2014, cutar Ebola ta barke a ƙasashen Afirka daban-daban. A nasa ɓangaren, shugaban tawagar ma’aikatan jinyar da ƙasar Sin ta tura zuwa Guinea karo na 23, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban asibitin Anzhen na Beijing, Kong Qingyu ya bayyana cewa, a wancan lokaci, likitoci ba su fahimci cutar sosai ba, sun dai san cuta ce kawai mai saurin yaduwa, amma babu wani takamammen magani.

Lokacin da cutar Ebola ta ɓarke a yammacin Afirka, ya zo daidai da lokacin da tawagar likitocin ƙasar Sin karo na 23 ke shirin kammala ayyukansu baki ɗaya a Guinea. Amma likitocin ƙasar Sin sun zabi su ci gaba da aiki a ƙasar.

Nas Wang Jing daga tawagar maaikatan jinyar ƙasar Sin karo na 24 tare da takwarorinta na Guinea

Kong Qingyu ya ce, ba tare da bata lokaci ba, tawagar ta tuntubi hukumomin lafiya na ƙasar Sin don neman samun taimako, da nazarin sabbin bayanan da aka turo daga ƙasar Sin, don fadakar da al’ummar Guinea kan ilimin kandagarkin cutar Ebola. Haka kuma a lokacin, an riga an kafa tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin karo na 24, masu shirin zuwa Guinea don samar da agajin jinya. Shugaban tawagar, mai ƙwararrun likitoci 19 daga asitibin zumunta na Beijing, Wang Zhenchang ya ce, bayan da cutar Ebola ta ɓarke, akwai ƙasashe da dama da suka janye jari da mutanensu daga Afirka, tawagarsa karo na 24 ita ma tana da zabi biyu. Wang ya ce, idan ba su je ba, tawagar da ta riga ta kammala aiki ba za ta iya dawowa ƙasar Sin ba, shi ya sa ya zama dole sabuwar tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin kashi na 24 ta tafi can ƙasar Guinea don daƙile annobar tare da al’ummar ƙasar.

A ranar 16 ga watan Agustar shekara ta 2014, kashin farko na tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin karo na 24 ƙarƙashin jagorancin Wang Zhenchang sun isa ƙasar Guinea, inda suka ƙaddamar da aikin daƙile yaɗuwar cutar Ebola ba tare da wani jinkiri ba. Baya ga aikin kula da masu kamuwa da cutar gami da ba su magani, ma’aikatan jinyar ƙasar Sin sun samar da horon kiwon lafiya ga takwarorinsu sama da 1700 na ƙasar Guinea, ciki har da akawun gwamnatin ƙasar, waɗanda suka canja ra’ayinsu tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen yaki da annobar Ebola a ƙasar.

Dangane da haɗin-gwiwar ƙasashen Sin da Guinea kuwa, wani muhimmin abun da ba za manta da shi ba shi ne, asibitin sada zumunta tsakaninsu, wanda aka fara amfani da shi tun a watan Afrilun shekara ta 2012. Sakamakon goyon bayan tawagogin ma’aikatan jinyar ƙasar Sin, an kara kafa sassa daban-daban a asibitin, abun da ya sa asibitin ya zama kan gaba a duk fadin ƙasar Guinea.

Wang Yu shi ne shugaban tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin da aka tura zuwa ƙasar Guinea karo na 25, kana mataimakin asibitin Tongren na Beijing. Wang ya bayyana cewa, lokacin da suka isa Guinea a watan Janairun shekara ta 2016, an kusan kawo ƙarshen yaɗuwar cutar Ebola, kuma ɗaya daga cikin muhimman ayyukansu a lokacin shi ne, taimakawa wajen ganin an gina sashin kula da masu fama da cututtuka masu tsanani, inda ma’aikatan jinyar ƙasar Sin suka fara horar da takwarorinsu na asibitin sada zumunta na Sin da Guinea, da nuna musu yadda za’a kula da masu fama da cututtuka masu tsanani a zahirance.

Tawagar maaikatan jinyar ƙasar Sin karo na 29 tare da likitocin ƙasar Guinea

A watan Satumbar shekara ta 2020, yayin da cutar mashako ta COVID-19 ke yaduwa a duk fadin duniya, ƙasar Sin ta tura tawagar ma’aikatan jinyarta karo na 28 zuwa kasar Guinea, wadda ke ƙunshe da kwararrun likitoci daga hukumar kiwon lafiya ta Beijing, da asibitin Xuanwu na Beijing, gami da cibiyar daƙile cututtuka masu yaɗuwa ta Beijing. Shugaban tawagar ma’aikatan jinyar ƙasar Sin karo na 28 da aka tura zuwa Guinea, Zhang Wei ya ce, kula da marasa lafiya a wurin ba abu ne mai wahala sosai ba, abu mai wuya shi ne yadda likitocin ƙasar Sin za su koyawa takwarorinsu na wurin fasahohin aikin jinya. Domin cimma wannan buri, likitocin ƙasar Sin sun bi hanyoyi daban-daban don inganta ƙwarewar likitocin Guinea. A ranar 19 ga watan Janairun shekarar da muke ciki, an kafa cibiyar kula da jijiyoyin dan Adam, da cibiyar kula da marasa lafiya daga nesa, gami da ɗakin gwaji na jijiyoyin dan Adam a asibitin sada zumunta na Sin da Guinea, al’amarin dake da babbar ma’ana ga ci gaban harkokin kiwon lafiya a ƙasar.

Yanzu asibitin sada zumunta na ƙasashen Sin da Guinea ya zama abin koyi ga muhimmin aikin faɗaɗa haɗin-gwiwar Sin da Afirka a fannin gina asibitoci, kuma dalilin jajircewar likitocin birnin Beijing, an ƙara raya asibitin sada zumunta na Sin da Guinea don zama cibiyar aikin jinya a yammacin Afirka, ta yadda ƙarin al’ummar nahiyar Afirka za su amfana.
Wani babban jami’in dake aiki a hukumar kiwon lafiya ta birnin Beijing mai suna Zhong Dongbo ya ce, tun lokacin da Beijing ta fara tura tawagar ma’aikatan jinya zuwa ƙetare a shekara ta 1968, ya zuwa yanzu, an canja ma’aikatan jinya daga tsoffi zuwa sabbi, amma abun da ba a canza ba shi ne daɗaɗɗen zumunci tsakanin al’ummomin Sin da Afirka, da kuma ra’ayi iri ɗaya, wato gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai ɗaya.