Ra’ayina a kan mas’alar almajirai da bara

Daga AMINU ƊAN ALMAJIRI

Har kullum ina yawan faɗa cewa, waɗanda ba su da Ilimi a kan abu idan suka ce za su yi bayani a kan abu, dole a samu rashin adalci cikin jawabin nasu. 

Jama’a ya kamata ku sani; ALMAJIRCI daban, sannan BARA daban. 

Da farko dai almajiri shi ne aka kawo shi wajan wani malami, domin ya samu karatun Alƙurani da sauran ilimai na addinin Musulunci. 

Wannan shi ne haƙiƙar almajiri. Irin wannan almajirin za ka samu idan za a kawo shi za ka ga Babansa ko Wakilin Baban nasa ya taho da kayan abinci. Sannan lokaci-lokaci yana zuwa ya kawo ziyara ga ɗansa domin ganin yadda abubuwa suke tafiya. 

Mai bara kuma shi ne, wanda iyayensa suka kawo shi birni karatu da sunan almajiri, amma a zahirin gaskiya ba almajiri ba ne. Uban ya kawo shi ne kawai don ya rage yaran da suke gabansa ne saboda ya tara garken ‘ya’ya bisa dalilin yawan aure-aure da yake yi. ga shi kuma ya kasa riƙe yaran nasa, balle ya ba su tarbiyya. To irin waɗannan yaran su ne ake kawo su wajen malami. Wani yaron ko gama mantawa da nonon uwarsa bai yi ba, sannan kuma ba abinci, ba cikakkiyar sutura. 

A qarshe babu kulawa ko kawo ziyara don ganin halin da yaron yake ciki. Waɗannan yaran su ne ga su nan duk kasuwa ko danja din titi idan ka je su za ka tarar, saboda su ne uwar kansu sannan uban kansu. Su za su nema wa kansu abinda za su ci, da inda za su kwana. Halal za su ci ko haram, duk iyayen yaran ba ruwansu. To irin waɗannan yaran wallahi ko ni na samu dama, tabbas idan an kama uban yaro kai tsaye sai na tabbatar an hukunta shi. Domin ba a wajabta masa yawan aure-aure ba, amma an wajabta masa dole ne ya kula da haƙƙin ‘ya’yan da ya haifa. 

Laifin malaman makarantun allo a fahimta ta shi ne, tunda sun san cewa wasu suna ɓata musu suna da sunan cewa su ma malamai ne, kamata ya yi su sanya hukuma a ciki wajen ganin an daƙile matsalar. 

Laifin al’umma kuma shi ne, har kullum idan matsala irin wannan wadda za ta shafi kowa idan ta faru, ba ma tunanin tantance tsaba da tsakuwa, sannan ba ma tunanin mene ne mafita. Kawai muna ɓata lokacinmu ne wajan ɓaɓatu a kafafen watsa labarai, amma babu wanda zai yi tunanin ta yaya shi da abokansa za su fara kawo gyara ko da a unguwarsu ne. Idan da kowa zai ajiye surutu a gefe, ya ɗauki gaɓaren kawo gyara tare da masu tunani irin nasa da suke kusa da shi, tabbas za mu samu ƙarancin matsaloli cikin wannan al’umma tamu. 

Ina mana fatan alkhairi tare da tuna mana cewa, almajiri daban, masu yin bara, daban! Amma mene ne mafita? Surutu kawai muka iya ba neman mafita ba!

Jiya na faɗa, yanzu ma zan sake faɗa, da yawa za a iya ɗaukar kwanaki a kafafen yaɗa labarai ana ta ɓaɓatu a kan wata matsala, amma da wahala ka ji ana vavatu akan ina mafita, ko kuma yaya za yi maganin matsalar? 

Almajiran nan ko muna so, ko ba ma so dai musulmai ne masu son koyon Ƙurani. Rashin adalci ne a kalli almajiri mai neman Ilimi da wanda bara yake da sunan almajiri a ce duk ɗaya suke. 

Sannan duk wannan abunda ake da yawa ba ku je inda haƙiƙar makarantar almajirai din suke ba, balle ku iya ba da bayani na gaskiya a kansu. Bari na ba da misali da abinda na gani da idona

Akwai wani ƙauye a cikin Kano ɗin nan da na je, sai na tarar da almajirai tare da ‘yan garin suna ta ƙwami na karatun Alƙur’ani, amma saboda yawansu, abin zama tare da shi kansa inda ake zaman sun yi ƙaranci, makarantar da tana da ɗalibai sun kai 300, azuzuwa 2 aka gina musu tun zamanin Shekarau, sai kuma rumfar kwano guda 1. a hankalce don Allah ta  ya ya wannan guri zai ɗauki waɗannan ɗalibai?

Shukran la fakhran, haka na yi ƙoƙari aka samu tabarmi kusan guda 10, muka sake komawa garin aka kai musu wannan gudunmawa. 

Al-muhimm a nan shi ne ba adalci ba ne, sannan ba dai-dai ba ne a ɗauki laifi a ɗora wa wanda ba mai laifi ba ne. Sannan matuƙar Mas’alar almajirai tana damun kowa, to ya kamata kowa a kansa ya yi niyyar taimakawa da abinda zai kawo ƙarshen matsalar. 

Malamai, Limamai, Shugabanni, Jami’an tsaro, alƙalai, lauyoyi, mawadata, ‘yan kasuwa maza da mata kowa yana da hannu wajen ganin an yi maganin matsalar barace-barace ɗin nan, sannan a ɗauke kalmar barace-barace ga almajirai na ainahi, a mayar da ita ga masu bara da sunan almajirai. Allah Ya sa mu dace.

Aminu ɗan Almajiri ya rubuto daga Kano.