Bambancin bara da almajiranci

Daga IBRAHIM MUHAMMAD MANDAWARI

Bari na ɗan yi tsokaci a kan bambancin da ke akwai tsakanin bara almajiranci. Ita Kalmar Almajiranci ta samo asali daga kalmar Larabci ne, duk da dai ma’anar da Larabawa suke ba ta ya sha bamban da yadda muka fassara ta a Hausa.

Almajiranci a Hausa na nufin tura ƙananan yara zuwa makarantun tsangaya waɗanda mukan ce ‘Gabas’ domin koyon karatun Al-Ƙurani. Wannan yana farawa daga matakin farko wato babbaƙu zuwa farfaru, zuwa haddatu sannan sai taƙara da tilawa. 

Hakazalika, ‘ya’yan wannan makaranta sukan fara da ƙaramin yaron da ba zai iya ko yi wa kansa tsarki ba, wanda ake kira kotso (pre- nursery) sannan sai Ƙolo (Nursery), sai kuma Titiɓiri (primary school), daga nan sai matakin zama Gardi (secondary school), sai kuma mataki na gaba wato; Malam (Tertiary institution); sai kuma Alaramma (university). Kazalika a cikin Jami’a ta Karatun Alƙur’ani irin na ƙasar Hausa, akan samu Gwani ko Mahiru (Academic Doctor.) daga  nan kuma sai uwa-uba wato, Gangaran (professor).

Duk waɗannan matakai ne na neman sanin Ƙur’ani a makarantun Tsangaya na ƙasar Hausa. Akasarin Malaman da ake taƙama da su a yau din nan, sai da suka bi waɗannan matakai sannan suka zama abin da suka zama. Hatta ɗalibanmu da suka kai ga cinye gasar masabaƙar Alƙur’ani mai tsarki ta Duniya, sai da suka fara da karatun tsangaya a birane ko a ƙauyuka kafin su kai ga iya Tajwidin Ƙur’ani da sanin ilimin tafsiri. 

A tsangaya, Alaramma ne Jagora kuma yana kula da karatun Almajiransa dare da rana. Misali, yakan tashi ɗalibansa tun bayan sallar Asuba su fara ƙwami, wato bitar karatunsu na Allo har zuwa hudowar rana. Daga nan sai ya ƙyale su zuwa kamar 11 na safe, sai  ƙanana daga cikinsu wato ƙolawa su je ga gidajen da ake aikensu cefane ko ɗebo ruwa da sauran aikatau, inda a wannan gida akan ba su ɗumamen tuwo da safe, sannan da daddare ma a ba su tuwon dare. Kenan ka ga ba sai sun yi bara ba.

Kazalika, waɗannan yara sukan yi rubutun sha domin kai wa ga iyayen ɗakunansu mata, wato gidajen da ake hulɗa da su. Sukan rubuta wa mata Lahaula ko Falaki da Nasi da makamantansu (wannan rubutu shi suke kira Darni). Kuma rubutun yakan cinye lokacin Ƙolo, ta inda ba zai samu lokacin yawace -yawace ba. Sannan bayan sallar La’asar, Malam yakan kaxo kan Almajirai (Kolawa da Gardawa) kowa ya ɗauko allonsa ya yi ta biyawa har gefin magariba, yayin da a wannan lokaci manyan Almajirai kan zauna darasu tare da Malam. 

Kazalika, bayan an yi magariba da Isha, sai a shiga yin karatu ta hanyar tilawa (wato karanta Ƙur’ani da ka) wanda suke kira (Ja dare). 

La’akari da yadda Malaman makarantun Allo ke ɗauke lokutan Almajirai, ya nuna cewa ba su da lokacin yawon bara ballantana yawon ta-zubar. Kai ko da lokacin damina ne, to almajirai na zuwa gonar Malam ne su yi noma da rana, sannan idan an yi girbi da su za a ci abincin gidan Malam. 

Amma yawon bara musamman na ƙananan yara, zamani ne ya kawo shi.  “Ko ɗan ƙanzo”  “ko ɗan Dago-dago” “Wahidin Mummunai” da sauransu shi ne za ka ga ƙananan yara cikin dauɗa da rashin tsafta da yunwa da kirci da tsumman kaya suna yawo kwararo-kwararo suna bara, har ma idan yunwa ta tambaye su za ka gansu kwance a gefen hanya ƙudaje na bin bakinsu. 

Dan haka, sai mu yi nazari da kanmu kuma mu dubi Allah, mu ga me ya dace da yaranmu; almajiranci domin sanin Alƙur’ani mai tsarki, ko zama cikin kaskanci?

Ya kamata dai mu sani cewa, idan mun kula da ‘ya’yan da muka haifa a cikinmu ta hanyar ba su tarbiyya, da ba su ilimi da kula da lafiyarsu da cusa musu aƙidar addini, kuma muka yi ko in kula da ‘ya’yan talakawwa to akwai ranar ƙin dillanci. 

A nan ina ganin alhakin iyaye da Hukumomi da Malamai da sauran al’umma shi ne kula da alƙibar yara masu bara a tituna. Allah ya sa mu dace.

Alhaji Ibrahim Mandawari shine Mai Unguwar Mandawari a Birnin Kano