Haihuwar yuyuyu babbar fitina ce a cikin al’umma – Sameerah Shinko

“Yawaitar ilimin mata zai kawo sauƙi ga matsalolin da suka addabi al’umma”

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Sameerah Bello Shinko haifaffiyar garin Sokoto da ke Arewacin Nijeriya ce.Ta yi ‘primary’ da Sakandire duk a cikin garin Sokoto. Sannan ta wuce Sokoto state polytechnic inda ta yi diploma a kan ‘Sciences laboratory technology’. Sannan ta sake koma wa Waziri Umaru polytechnic Birnin Kebbi inda tayi HND a kan Microbilogy/biochemistry. yanzu kuma tana karatun Post graduate diploma a kan ‘Environmental and public’ a Bayero university Kano. Sameerah fitacciyar marubuciya ce sannan ‘yar rajin kare haƙƙin bil adama musamman ma mata. Sunanta ya yi tambari a ‘social media’ a kan hakan. Hirar ta da Manhaja ta taɓo batutuwa mabambanta. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ki gabatar da kan ki ga masu karatunmu.
SAMIRA: Sunana Samira Bello Shinko, ‘yar asalin Jihar Sokoto. An haife ni a garin Sokoto kuma na yi karatuna har zuwa matakin diploma duk a Sakkwaton, kafin in yi aure a Jihar Zamfara, ina da yara huɗu yanzu.

Dangane da batun karatu, waɗanne makarantu kika halarta?
Na fara primary a Yakubu Mu’azu Sciences Model primary school Sokoto,in da na ƙarasa a Unity comprehensive school Sokoto. Na yi karatun Secondary a Asma’u girls Islamic school Sokoto, kafin na wuce zuwa Sokoto state polytechnic inda na yi diploma a kan ‘Sciences Laboratory Technology’. Bayan mun rabu da maigidana, na koma Waziri Umaru polytechnic Birnin Kebbi inda na yi HND a kan ‘Microbiology/Biochemistry’. Na yi bautar ƙasa a Jihar Zamfara, yanzu kuma ina karatun ‘Post graduate diploma’ a kan environmental and public a Bayero university Kano.

Ki na cikin masu gudanar da ƙungiyoyin tallafi ga al’umma. me za ki ce a kan haka?
To, a matsayina na mace kuma uwa, na fahimci ba iya cikin gida ba ne kawai muke da gudunmuwar da zamu bayar ba, shi yasa na fara aiki da irin waɗannan ƙungiyoyin masu zaman kansu, domin tallafa wa al’umma musamman mata, yara ƙanana da kuma gajiyayyu. Kuma muna taimaka wa ne kan abubuwan da suka shafi ilimi, tazarar haihuwa, kariya da wayar da kai daga rashin lafiyoyi kamar zazzaɓin cizon sauro da sauran su. Sannan muna bada tallafi ga marayu da yan gudun hijira.

Dangane da harkar sana’o’i fa?
Ai yanzu muna zamanin da kai ya waye, ba wanda zai dogara da iya aikin gwamnati, dole sai an haɗa da yan sanao’in hannu. Kuma ga shi zamani ya zo mana da hanyoyin sadarwa na zamani da za ka iya tallata hajarka kana daga gida. Ni ma duk ayyukan da nike ba su hana ni siyar da kaya ba ta ‘internet’, kuma alhamdu lillah har rijistar an yiwa ‘company’ na da CAC.

Waɗanne irin matsaloli kuka fi fuskanta a yayin ayyukanku na tallafa wa al’umma?
Babbar matsalar da muka fi fuskanta shine tirjiya daga jama’a, sai su ce wai mu ‘yan kwangilar Yahudawa ne. Misali, akwai ƙungiyar da na ke yiwa aiki mai suna Marie stopes international, sun taimaka wa al’umma ne da hanyoyin tazarar haihuwa abinda muke cewa ‘family planning’ a Turance, kuma kyauta ne duk hanyar da ka zava. Amma sai a ce muna son a daina haihuwa, abinda Annabi ya ce, a haifa dan ya yi alfahari da al’umar sa. Sannan idan muka duba ai akwai hadisin Manzon Allah (S.A.W) da yake cewa, “ƙarancin iyali ɗaya daga cikin sauƙi ne ga Mumini.” Ma’ana idan mutum yana da karancin iyali zai samu sauqin ɗawainiya da su. Don haka mutum ya tara iyali ya kasa ɗaukar ɗawainiyarsu lallai ba farar dabara ba ce ba. Gaskiya irin waɗannan matsalolin muna samun su sosai, sai kuma ɓangaren irin tallafin da ake ba wa ‘yan gudun hijira wani lokaci mutanen gari na shiga cikinsu karɓan tallafin wanda hakan bai dace ba, su sun bar mahaifarsu da komai na su suna buƙatar taimako, amma sai a zo ana karɓe ɗan tallafin nasu.

Matsalar yi wa mata fyaɗe da cin zarafinsu ta ɓangarori da dama sai ta’azzara take. Me za ki ce kan haka?
Wannan abin ya dazɗe yana ci min tuwo a ƙwarya, saboda duk da wayar da kai da ƙorafi da ake a kan abin, bai yi sauƙi ba sai ƙaruwa da yake. Kuma abu biyu zuwa uku ya janyo hakan, rashin hukunta masu laifi idan an kama su, sakacin iyaye da kuma yawan yaɗa ɓarnar a kafafen labarai. Hakan ya ba wa wasu damar aikata irin laifin. To idan ba a yi maganin wannan abubuwan uku ba, ba ganin ƙarshensa za a yi ba.

Wane kira za ki yi dangane da bai wa ‘ya’ya mata damar yin karatu mai zurfi?
To, ilimi dai shine gishirin zaman duniya, kuma ita mace ita ce ginshiƙin al’umma. Idan aka samu mata masu ilimi, mafi akasarin matsalolin da ake fuskanta za su kau. Saboda mace mai ilimi baza ta kasa wurin ba wa yaranta tarbiyya mai inganci ba. Kamar dai yanda ake faɗa, idan ka ilmintar da mace ɗaya, kamar ka ilmintar da al’umma ne. Don haka, ina kira ga iyaye da su mayar da hankali wurin ganin sun ilmintar da ‘ya’yansu mata, a ba su dama suyi ilimi mai zurfi. Ba kuma iya ilimin boko kaɗai na ke magana ba, har da na addini da iya mu’amala da zamantakewa. Allah yasa mu dace.

Madalla. Mun gode Hajiya.
Ni ma na gode sosai. Allah ya taimake ku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *