Dalilan Kannywood na ƙaurace wa bikin ZUFF 2022

Daga BASHIR ISAH

Gamayyar ƙungiyoyin masu shirya finai-finai a masana’antar Kannywood ƙarƙashin jagorancin MOPPAN da AFMAN sun aike wa Ministan Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed buɗaɗɗiyar wasiƙa suna masu sanar da shi dalilansu na ƙaurace wa bikin baje-kolin fina-fina da aka fi sani da ZUFF a taƙaice na 2022.

Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun Dr. Ahmad Muhammad Sarari na MOPPAN da Alhaji Sani Sule Katsina na AFMAN, ta nuna waɗanda lamarin ya shafa sun ƙi halartar bikin ne saboda nuna musu wariya da aka yi.

Hukumar Kula da Harkokin Fina-finai na ta Ƙasa (NFC), ita ce mai shirya wannan biki duk shekara, wanda a halin yanzu bikin bana ya kankama a Abuja.

Sanarwar manema labarai da ta sa ami sa hannun sakataren MOPPAN na ƙasa, Al-Amin Ciroma, ta nuna dalilan da suka sanya ‘yan fim ɗin na Arewa ƙaurace wa bikin, ciki har da yadda aka sanya lokacin bikin daidai da ranar sallah, rana mai muhimmanci ga Musulmin duniya.

Haka nan, sun yi ƙorafin duk da NFC ta nada shugaban MOPPAN na ƙasa tare da wasu a matsayin waɗanda za su kula da yankin Kaduna da Kano dangane da shirye-shiryen bikin ZUFF na bana, duk da cewa sun yi aikin da aka ɗora musu amma har zuwa lokacin da aka aika wa Minista Lai da wasiƙa NFC ba ta ce musu komai ba alhali tana yi da takwarorinsu na Kudu, sannan ta yi ta yayata cewa da Kannywood ake komai.

Kazalika, sanarwar ta nuna yadda NFC ta sanar da jigo a Kannywood, Alhaji Ibrahim Mandawari cewa, yana ɗaya daga cikin waɗanda za a karrama yayin bikin amma daga bisani aka sanar da shi an cire sunansa ba tare da wani ƙwaƙƙwaran dalili ba. Yayin da aka bar sunayen waɗanda a aka zabo daga sauran sassa.

Bisa waɗannan dalilai ne gamayyar ‘yan fim daga Arewa suka yi fatan Minista Lai ya sa baki cikin badaƙalar don samar da maslaha.

Sanarwar ta ce, Kannywood ita ce masana’antar shirya fina-finai a Arewa wadda ke da zama a Jihar Kano. Masana’antar da take ba da gudunmawa wajen samar da aikin yi, koya wa matasa iya dogaro da kai, fadakarwa da dai sauransu.