Wani kamfanin ƙasar Sin ya ƙaddamar da gidauniyar tallafawa al’umma a ƙasar Saliyo

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Kamfanin “Leone Rock Metal Group” na kasar Sin, mai aikin hakar ma’adanai a ƙasar Saliyo, ya sanar da ƙaddamar da gidauniyar bunƙasa ci gaban al’ummar ƙasar.

Kamfanin ya ce zai rika keɓe kaso ɗaya bisa ɗari na ribar da yake samu a duk shekara, wajen tallafawa al’ummun gundumar Tonkolili, dake lardin arewacin ƙasar inda yake gudanar da ayyukansa.

Da yake ƙarin haske game da hakan yayin ƙaddamar da gidauniyar, babban jami’in kamfanin Zhao Ting, ya ce har kullum kamfaninsa a shirye yake, da ya ba da gudummawa ga manufar raya masana’antun ƙasar Saliyo, tare da bunƙasa rayuwar mazauna wuraren da yake gudanar da ayyukansa.

A nasa ɓangare, shugaban ƙasar Saliyo Julius Maada Bio, ya bayyana matakin da kamfanin ya dauka a matsayin mai matuƙar muhimmanci, a fannin bunƙasa yankin da yake gudanar da ayyukan sa.

Mai Fassarawa: Saminu

By Editor