Xi Jinping ya gana da Michelle Bachelet

Spread the love

Daga CMG Hausa

Shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, ya gana da babbar jami’ar hukumar MƊD mai lura da kare haƙƙoƙin bil adama Michelle Bachelet ta kafar bidiyo a yau Laraba a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya yi maraba da ziyarar Bachelet a ƙasar Sin, kuma ya nuna cewa, ƙasar Sin tana son aiwatar da shawarwari, da haɗin gwiwa tare da dukkan sassan duniya bisa daidaito da mutunta juna, don sa ƙaimi ga bunƙasuwar ayyukan kare haƙƙin bil’adama na ƙasa da ƙasa, tare da amfanar jama’ar ƙasashe daban daban.

A cewarsa, yanzu haka abu mafi mahimmanci shi ne a yi abubuwa guda huɗu yadda ya kamata. Na ɗaya shi ne riko da tsarin da ya shafi mutane, wato mayar da al’umma gaban komai. Na biyu mutunta hanyar ci gaban ‘yancin dan Adam na kowace ƙasa. Na uku yin la’akari da kowane irin haƙƙi na dan adam. Na huɗu, ƙarfafa tsarin kula da haƙƙin dan Adam na duniya.

A nata ɓangaren, Bachelet ta ce, za ta yi mu’amala kai tsaye sosai tare da gwamnatin ƙasar Sin, da masu aiki a sassa daban daban na ƙasar. Ta kuma bayyana imanin cewa, wannan ziyara za ta taimaka mata wajen kara fahimtar ƙasar Sin sosai.

Ta ce hukumarta na son ƙarfafa cudanya da ɓangaren ƙasar Sin, da tattauna da haɗin gwiwa, kana da yin ƙoƙari tare, don sa ƙaimi ga ci gaban ayyukan kare haƙƙin bil’adama na duniya.

Mai fassara: Bilkisu Xin

By Editor