Ƙasashen Yamma na “fakewa da guzuma domin harbin karsana”

Spread the love

Daga SAMINU HASSAN

Sau da yawa wasu ƙasashen yammacin duniya, suna danganta ci gaban da suka samu da biyayyar su ga tsarin dimokaraɗiyya, da salon mulki mai alaƙa da hakan.

Ga misali, ƙasashen Amurka da Birtaniya, da ƙasashen tarayyar Turai, na yayata cewa dimokaraɗiyya ce ta haifarwa al’ummunsu da daidaito wajen samun damammakin kyautata rayuwa da ‘yanci, kuma hakan ne ya ba su damar bunƙasa tattalin arzikin su yadda ya kamata. Don haka ne suke tsananin fatan yayata salon jagorancin su zuwa sauran sassan duniya.

To sai dai kuma, masu sharhi kan al’amuran siyasar duniya da dama, na ganin cewa, wannan iƙirari ba gaskiya ba ne. Hasali ma ci gaban da dama daga ƙasashen yamma, ya dogara ne ga yadda gwamnatocinsu na can baya, suka ci da gumin ƙasashe masu rauni. Hakan na iya ƙara bayyana, idan aka yi waiwaye kan yadda irin waɗannan kasashen yamma suka bautar da wasu al’ummun ƙasashen Asiya, da na Latin Amurka, da na Afirka, suka kuma wawure albarkatun su.

Ko shakka babu, yayata dimokaɗiyya salon ƙasashen yamma, wata dabara ce ta yaudara, da “fakewa da guzuma a harbi karsana”. Hanya ce ta samarwa kai moriyar tattalin arziki, da sarrafa ikon ƙasashe musamman masu rauni.

Abubuwan da suka faru bayan yakin duniya na biyu, na mamayar ƙasashe da ƙarfin soji, da mulkar kasashe ta amfani da ‘yan koren ƙasashen yamma, da rura wutar yaƙe-yaƙe, da kifar da zababbun gwamnatoci, da kafa hukumomin kuɗi masu dorawa ƙasashe bashi mai ruwa fiye da kima, dukkanin su shaidu ne, na yadda waɗannan irin manyan kasashen yammacin duniya suka mayar da dimokaraɗiyya wani makami na ci da ceto!

Daga ƙarshe, idan har waɗannan ƙasashen yammacin duniya na da burin aiwatar da dimokaraɗiyya mai inganci, ya zama wajibi su kiyaye, tare da martaba bambance-bambance da ke tsakanin ƙasashe, shiyyoyi, al’adu, da nau’o’in dimokaraɗiyya dake iya dacewa da al’ummu mabambanta. Kaza lika, ya zama wajibi su yi watsi da salon dimokaraɗiyyar yake yake.

Bugu da ƙari, lokaci ya yi da za su rungumi al’ummun duniya bisa tausayi da jin ƙai, wato dai su rungumi salon dimokaraɗiyyar al’umma, wadda za ta haifar da alfanu, da damar cin gajiya ga al’ummun ƙasashe musamman matalauta, ta yadda ba za a bar kowa a baya ba!

By Editor