An yi kisa a wurin zaɓen fitar da gwani na PDP a Bayelsa

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Bayelsa da ke Kudu maso Kudancin Nijeriya, Douye Diri, ya yi Allah wadai da kisan wani mutum mai suna Michael Isaiah.

Lamarin ya faru lokacin da jam’iyyar hamayya ta PDP ke gudanar da zaɓen fidda gwani na ‘yan takarar kujerun majalisa a mazaɓar Ogbia da ke garin a Ƙaramar Hukumar Ogbia.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Kola Oredipe, ya rattava wa hannu ya ce ɓatagari ne suka yi kisan domin tayar da zaune tsaye da haddasa tashin hankali a zaɓen fidda gwanin da aka yi a jihar.

Gwamnan ya yi kira ga jami’an tsaro su gudanar da bincike kan kisan, da tabbatar da an kama waɗanda suke da hannu akai, don fuskantar shari’a da hukuntasu daidai da laifinsu.

Gwamna Diri dai ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin, da jaddada musu zai tabbatar da an hukunta waɗanda suke da hannu a lamarin.

An kashe matashin mai suna Michael Isaiah da aka fi sani da suna Tompolo ba tare da ya aikata komai ba.

By Editor