Daga BASHIR ISAH
Babbar Kotun Abuja ta ba da umarnin a tsare tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, karkashin kulawar hukumar EFCC a bisa zargin badaƙalar biliyan N2.9.
Alƙalin kotun, Inyang Ekwo ne ya ba da umarnin hakan a ranar Litinin a Abuja.
EFCC ta gurfanar da Okorocha da Chinenye tare da wasu kamfanoni me bisa tuhumar laifuffuka 17 masu alaƙa da almundahanar biliyan 2.9.
Aƙali Ekwo ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Talata inda kotun za ta saurari buƙatar belin da Okorocha da Chinenye suka gabatar.
Kamfanonin da lamarin ya shafa sun haɗa da: Naphtali International Limited da Perfect Finish Multi Projects Limited da Consolid Projects Consulting Limited da Pramif International Limited da kuma Legend World Concepts Limited.
Tsohon gwamnan kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar APC, ya faɗa a komar EFCC ne a ranar Talata, 24 ga Mayun 2022.
Da farko ɗan siyasar ya nemi kotu ta ba shi beli don ba shi damar halartar zaɓen fidda gwani na jam’iyyarsu wanda aka shirya gudanarwa tsakanin 29 da 30 ga Mayu kafin daga bisani aka ɗage zaɓen zuwa tsakanin 6-8 ga Yunin 2022.
