2023: Ba za ka taɓa zama shugaban Nijeriya ba, Ƙungiyar Ibo ga Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar ƙungiyar siyasa da zamantakewar Igbo, Ohanaeze Ndigbo, ta ce ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ba zai taɓa zama shugaban Nijeriya ba.

Ohanaeze ta bayyana hakan ne a lokacin da take yin tir da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP wanda ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Ƙungiyar ta bayyana zaɓen a matsayin wani tsari na rashin gaskiya da almundahana wanda ’yan Arewa marasa kishin ƙasa suka sa ido a kan Kudancin ƙasar nan.

Sakatare Janar na ƙungiyar Ohanaeze, Mazi Okechukwu Isiguzoro, ya jaddada cewa Igbo za su tada Atiku, ya ƙara da cewa za a yi watsi da yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a yankin Kudu maso Gabas.

Sun ce an mayar da PDP jam’iyyar Arewa.

A cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai, Isiguzoro ya koka da yadda ‘yan ƙabilar Igbo suka shirya ficewa daga zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na PDP.

Ya ce: “Abin mamaki ne a ce PDP ta zama jam’iyyar siyasa a yankin Arewa, inda Dakta Iyocha Ayu ya zama shugaban PDP, Walid Jubril a matsayin shugaban BOT da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2023.

“PDP ta cika barazanarta na mayar da ƙabilar Igbo baya a 2023 kuma za mu mayar musu da martani a hankali.

“Wani ɗan Arewa, Sanata David Mark ne ya sa ido a kan tsarin da aka ƙulla da ‘yan ƙabilar Igbo daga PDP. Sakamakon babban taron jam’iyyar PDP na 2022 zai zama dakatar da nonon ƙuri’un Igbo da wata jam’iyyar da ta kashe burin Igbo.

“Muna jiran zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya yanke hukunci na ƙarshe kan ko ‘yan ƙabilar Igbo za su shiga zaɓen 2023 ko a’a.

“Za a yi adawa da Atiku Abubakar a Kudu maso Gabas, kuma babu wani ɗan ƙabilar Igbo da ake sa ran zai yi kambun zaɓen Atiku a Gabas.

“Babu wanda zai yi kasadar yi wa Atiku kamfen a Gabas tunda yanzu PDP ta zama jam’iyyar siyasar yankin Arewa.

“Atiku ba zai samu ‘yan ƙabilar Igbo su mara masa baya a 2023 ba, ba zai iya zama shugaban ƙasar Nijeriya a 2023 ba.

Ndigbo za su kara da PDP da Atiku Abubakar a matsayin kyauta ga rashin godiyar PDP da rashin gaskiya ga Igbo.”

By Editor