CAN ga hukumomin tsaro: Dole ku kamo masu hannu a kashe Musulma a Anambara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya, CAN, ta buƙaci ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro da su kamo masu hannu a kisan wata Musulma mai juna biyu da aka bayyana sunanta da Fatima da ’ya’yanta huɗu a jihar Anambra.

Ƙungiyar kiristocin ta bayyana mutuwarsu a matsayin abin da ba za a amince da ita ba kwata-kwata, rashin gaskiya kuma abin zargi ne, ta kuma buqaci gwamnati da ta ɗauki matakin hukunta masu laifin.

Shugaban CAN, Rabaran Dr Samson Ayokunle, a wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Fasto Adebayo Oladeji, ya kuma yi kira ga jiga-jigan siyasa, malaman addini da sarakunan gargajiya na cire Ndigbo da su yi galaba a kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Gabas, a wani bangare na ƙasar don dakatar da zubar da jini da tashin hankali a yankin.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta yi Allah wadai, da kakkausar murya, kisan gilla da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka yi wa matar aure Fatima da ’ya’yanta huɗu da ba su ji ba ba su gani ba, tare da neman a yi musu adalci a yayin da ta yi kira ga jami’an tsaro da su kamo masu hannu a cikin aika-aikar domin kawo ƙarshen kashe-kashen rashin hankali a ƙasar.”

“Wannan laifin ba abin yarda ba ne, rashin gaskiya kuma abin zargi ne ga CAN da duk masu tunani. Muna kira ga jami’an tsaro da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ke kansu.

“Yanzu masu aikata laifin suna aiki ba tare da wani hukunci ba, yayin da waɗanda ake sa ran za su dakatar da su ko kuma a kama su sun nuna ba su da ƙarfi. Wannan ba za ta iya zama ƙasar mafarkin waɗanda suka yi gwagwarmayar kwato ma ta ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka ba.

“Abin takaici ne cewa babu inda za a sake samun kwanciyar hankali a qasar nan, domin masu kisa, ’yan fashi, ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane suna ta kai hare-hare a kowane lungu da saƙo na ƙasar nan, kuma duk abin da gwamnati za ta iya yi shi ne ta fitar da sanarwa lokaci-lokaci tana yin Allah-wadai da su ba tare da wani ko wata ba, da kuma yanke hukunci don gurfanar da masu laifin a gaban kotu.

“CAN ta yi kira ga shugabannin masu fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOBs) da su dakatar da waɗannan miyagun laifuka da nufin neman ’yancin kai.

“Shin suna gwagwarmayar don neman ƙasa ne na matattu ko masu rai? Su sani cewa laifukan da su ke aikatawa ba ya taimakawa lamarin shugabansu Nnamdi Kanu. Kada su mayar da yankin Kudu maso Gabas zuwa ga ‘Kufai’ domin maslahar Ubannin da su ka kafa ƙasar nan waɗanda suka fito daga shiyyar.

“Ayyukan da suke yi ba wai kawai suna ba wa Ndigbo suna ba ne amma suna haifar da yanayi na yaƙin ƙabilanci da addini. Shin ƙungiya mai hankali za ta kasance tana aikata laifuka irin wannan?

“Muna kira ga jiga-jigan siyasa, malaman addini da sarakunan gargajiya na Ndigbo da su yi nasara a kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Gabashin ƙasar nan don dakatar da zubar da jini mara amfani da tashin hankali da su ke haifar da faɗuwar tattalin arziki da walwala a yankin.

“CAN ta jajantawa duk waɗanda aka kashe a kashe-kashen rashin hankali musamman dangin Fatima da kuma dan majalisar dokokin jihar Anambra da aka kashe kwanan nan, Okechukwu Okoye,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *