Sanatan APC a Legas ya lashe tikitin tsayawa takarar Sanatan Ogun

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sanata mai wakiltar Legas ta Yamma, Sanata Solomon Adeola wanda aka fi sani da Yayi ya lashe tikitin jam’iyyar APC na tsayawa takarar Sanatan Jihar Ogun ta Yamma bayan ya yi wani gagarumin yunƙuri daga Jihar Legas zuwa Jihar Ogun.

Sanata Adeola ya samu tikitin tsayawa takarar jam’iyyar APC ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata a wajen zaɓen fidda gwani da jami’an jam’iyyar suka gudanar a ɗakin taro na Orona da ke Ilaro, hedikwatar ƙaramar hukumar Yewa ta Kudu a jihar.

A cewar jami’in zaɓen fidda gwani, Dapo Adekoya, Sanata Adeola ya samu ƙuri’u 294 inda ya kayar da ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar majalisar dattawa, Tolu Odebiyi, wanda ya samu ƙuri’u sittin.

Sanata Adeola bayan kasancewarsa ɗan majalisar wakilai ya tsaya takarar Sanatan Legas ta Yamma a shekarar 2015 kuma aka sake zaɓensa a matsayin Sanata a 2019.

A 2023, Sanata Adeola wanda ya samu nasarori da dama a siyasance a jihar Legas yanzu ya koma jihar Ogun domin cigaba da tafiyar siyasarsa, zai fafata da jam’iyyun adawa domin ya zama Sanatan Ogun ta Yamma a zaɓe mai zuwa.