Yadda wata babbar dillaliyar miyagun ƙwayoyi a Delta ta shiga hannu

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta yi nasarar cafke wata mata mai shekaru 59, wadda aka tabbatar ita ce shugabar dillalan muggan ƙwayoyi a Jihar Delta da maƙwabtanta.

Premium Times ta rawaito cewa: Matar mai suna Bridget Emeka, an fi sanin ta da suna Mama. An kama ta ne a ranar Lahadi, a wani danƙareren gidanta da ke garin Warri a jihar Delta.

Kakakin yaɗa labaran NDLEA, Femi Babafemi ne ya sanar da haka a ranar Talata a Abuja.

NDELA sun zargi Mama da riƙa yin amfani da kantamemen gidanta dake kan Titin Favour, Unguwar Otukutu da ke yankin Effurun a Warri ta na ta dafa sankacen hodar koken da sauran muggan ƙwayoyi ta na raba wa dillalanta.

A lokacin da aka kama ta, jami’an NDLEA sun tarkata har da ma’aikatan da makusanta su 9 duk suka yi awon gaba da su.

NDLEA ta ce an samu nasarar yin wannan samamen kamun manyan ‘yan ƙwaya tare da tafiya da sojoji wajen yin kamen.

Babafemi ya ce gidan Mama ƙaton gida ne da masu tu’ammali da wayoyi ke kwana kuma ana amfani da gidan a matsayin wurin tara muggan ƙwayoyi ana rarraba wa manyan diloli a cikin Warri.

Baya ga muggan ƙwayoyi da aka kama a gidan, an samu bindiga 1 mai harsasai 15.

“An samu takardun bayanai, motoci biyu, wayoyin salula da sauran tarkacen wuraren da ake zuba ƙwayoyi da ledojin naɗe ƙwaya duk a cikin gidan. Da zarar an kammala bincike, za a maka tu a kotu.