Yadda tsananta haraji ga kamfanonin sadarwa ya jawo matsalar sabis ɗin layukan waya a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Rahotanni sun nuna cewa, tsananin yawan harajin da gwamnatin Nijeriya take tafka wa kamfanonin sadarwa shi ne ummul’aba’isin na rashin ƙarfin sabis ɗin layukan waya a ƙasar nan. 

Wannan rahoto yana ƙunshe ne a wani rahoto da  SB Morgen suka  haɗa. 

Rahoton ya bayyana cewa, kamfanonin sadarwar suna azabtuwa daga haraji da ya zarta ƙa’ida da gwamnatin Nijeriya take ta lafta musu. Rahoton ya bayyana cewa, a yanzu haka akwai haraji iri daban-daban har kala 40 wanda kamfanonin sadarwa suke biya a Nijeriya.

Sai dai inda matsalar take a cewar rahoton, wannnan gingimemen haraji shi ya haifar da samun matsalar sabis a layukan wayoyi a Najeriya. 

Domin bayan tafkeken harajin, akwai wasu lokuta da gwamnatin kan sa jami’an tsaro su garƙame ofisoshin kamfanonin sadarwar su hana su shiga ko da zuba mai ne ko yin wani aiki, idan har ba su biya haraji ba. Wannan ma ya taimaka wajen rashin samun sabis. 

Wannan a cewar binciken al’amari ne da yake jawo koma-baya a harkar kasuwanci har da ƙarfin arziki na ƙasa na cikin gida.