Almundahana: EFCC ta cafke Yari bisa zargin alaƙarsa da badaƙalar Akanta-Janar

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa (EFCC), ta kama tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari bisa nasabarsa da binciken da hukumar ke kan gudanarwa a kna dakataccen Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris.

EFCC ta cika hannu da Yari ɗin ne a ranar Lahadi a gidansa da ke Abuja bayan da ya lashe zaɓen fidda gwanin APC inda ya zama ɗan takarar sanata na jam’iyyar a Shiyyar Zamfara ta Yamma a zaɓe mai zuwa.

Tun a ranar 16 ga Mayu Idris, ya faɗa a komar EFCC inda ake bincike a kansa kan zargin wawushe biliyan N80 daga aljihun gwamnati.

Binciken EFCC na zargin an haɗa baki da Yari wajen sace kuɗaɗen gwamnatin.

Majiyarmu ta ce an gano wata harƙalla abar zargi wadda ta gudana tsakanin Idris da Yari da ta kai ta kuɗi biliyan 20.