Yadda Kwankwaso ya taya Gwamna Wike kiciniyar kayar da Atiku a zaɓen PDP – Rahoto

Dagana AMINA YUSUF ALI

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon gwamnan Kano, Gwamna Kwankwaso ya amshi kuɗaɗe daga Gwamnan jihar Ribas, Wike, don raba wa daliget na Kano a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP, inda SaharaReporters ta ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya amshi kimanin Dalar Amurka 15,000 ga kowanne daliget na Kano.

Haka zalika, ya ɓoye daliget na Kano su 44 a wani otal, domin shirya wa nasarar ɗan takarar shugabancin ƙasar nan a PDP, Wike a zaɓen fidda gwanin.

Wata majiya ta bayyana wa Sahara Reporters cewa, Kwankwaso ya amsar wa kowanne daliget na Kano guda ɗaya Dalar Amurka $15,000 daga wajen Gwamnan Ribas kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa Wike. Sannan kuma ya girke wasu a daliget na ƙasa guda 44 a wani ɓoyayyen otal.

Shi dai tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ya bar jam’iyyarsa ta PDP ne a watan Maris ɗin da ya gabata, amma duk da haka ya cigaba da yin ɓoyayyiyar alaƙa da Nyesom Wike, ɗaya daga cikin ‘yan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP.

Wato kenan duk da ficewarsa daga jam’iyyar PDP, hakan bai sa ya daina alaƙa da wasu manya a jam’iyyar PDP ba, kamar yadda jaridar ta yanar gizo ta riwaito.

Wata majiya ta bayyana wa Sahara Reporters a ranar Asabar ɗin da ta gabata cewa: “Kwankwaso ya amsar wa kowanne daliget na Kano guda ɗaya Dalar Amurka $15,000 daga wajen Gwamnan Ribas kuma ɗan takarar shugaban ƙasa Wike. Sannan kuma ya girke wasu a daliget na ƙasa guda 44 a wani ɓoyayyen otal.”

Haka zalika, tun a safiyar Asabar da ma kuma Sahara Reporters ta rawaito yadda tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya Atiku Abubakar, da Wike, da wasu daga cikin sauran zawarawan kujeraun shugabancin ƙasar suka yi ta wasa da dala ga daligets don samu yin nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.

Rahotanni sun bayyana cewa, kowanne daligets ya tashi da cin hanci na kusan $55,000 domin kawai a sayi ƙuri’unsu. Kuma daliget ɗin sun tasamma guda 811.

Wato akwai daliget guda 774 daga kowacce ƙaramar hukuma mutum ɗaya a faɗin tarayyar ƙasar nan. Sannan kowacce jiha ma da Abuja tana da daliget guda-guda. Sannan kuma mutane masu buƙata ta musamman ma suna da nasu wakilan.

Wata majiya daga cikin jam’iyyar ta bayyana wa SaharaReporters a ranar asabar ɗin da ta gabata cewa, Tun daga Atiku, zuwa Wike, zuwa tsohon shugaban majalisar zartarwa, Bukola Saraki da Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, dukkansu rigegeniya suke yi wajen watsa dubunnan daloli ga daliget-daliget don samun kai wa gaci. Abin dai ya zama iya kuɗinka, iya shagalinka.

Kowanne daliget inji wata majiya ya samu Damar Amurka $55,000. Wato gwari-gwari; Wike, Dala 15,000; Atiku, Dala 20,000; Saraki, Dala 10,000, Tambuwal, Dala 10,000”.

Kuma a cewar majiyar ba tun yau abin ya fara ba. Domin tun watannin baya ‘yan takarar suke ta yawo a faɗin ƙasar nan don yin toshi ga daliget-daliget ɗin don jan ra’ayoyinsu.

Wannan ya taimaka ƙwarai wajen sulalewar jikin wasu ‘yan takara da suka tsorata suka janye ganin faɗan ya fi ƙarfinsu. Misali irin su Mohammed Hayatu-Deen, wanda ya janye daga takarar a safiyar ranar zaɓen fid da gwanin.