Nasarar Atiku a zaɓen fidda gwani ta jefa APC cikin ruɗani – Urzo Kalu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan Jihar Abiya, Orji Uzor Kalu ya gargaɗi Jam’iyyar APC ta yi karatun ta natsu wajen zaɓen fidda ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar.

Da yake miƙa saƙon taya Atiku murnar nasarar da ya yi a zaɓen fidda gwani na Jam’iyyar PDP, Kalu ya ce kada APC ta kuskura ta tsaida wani ɗan Kudu ɗan takaran ta.

”Idan har ba ritayar dole APC take so ta tafi ba a siyasa, toh ta zaɓi ɗan Arewa ne ya yi mata takarar Shugaban Ƙasa tunda wuri. Kuma Ahmed Lawan ne ya fi dacewa.

”Dalili kuwa shine, Ahmed Lawan ɗan yankin Arewa maso Gabas ne, yankin da Atiku ya fito. Hakan zai sa APC ta yi tasiri a zaɓen da za a yi a 2023.”

Kalu ya ce a halin da ake ciki yanzu sai an sake yin nazari mai zurfi a lissafin da ake yi a jam’iyyar.

Idan ba a manta ba tsohon mataimakin shugban ƙasa Atiku Abubakar ne ya yi nasara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka yi ranar Asabar a Abuja.

Atiku ya samu ƙuri’u 371, inda ya doke abokanan takararsa, Nysom Wike, Bukola Saraki, Bala Mohammed, Emmanuel Udom na jihar Akwa-Ibom sai kuma Aminu Tambuwal da ya janye wa Atiku dab da za a fara kaɗa ƙuri’a.