Ranar Yara: Ma’aikatar Mata ta sha alwashin samar da kyakkyawar Rayuwa ga Yara – Dr. Zahra’u

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

A duk ranar 27 ga watan Mayun kowace shekara ne dai ake gabatar da ranar Yara ta Duniya wato World Children Day, taron na bana dai shi ne: “Samar da kyakkyawar makoma ga kowane Yaro”.

Jihar Kano ma ba a barta a baya ba wajen aiwatar da wannan bikin, inda Gwamnatin jihar Kano tare da Ma’aikatar Mata da ci gaban al’umma ta gabatar a gidan Gwamnatin jihar, Kano.

Tun da farko a jawabinta, Kwamishinar Mata da Cigaban Al’umma ta Jihar Kano, Dr. Zaharau Muhammad, ta bayyana muhimmancin wannan rana da kuma tasirin da ta ke da shi a tsakanin yara.

Ta ce, “Ma’aikatar Mata da Cigaban Al’umma da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin cigaban al’umma da ƙungiyoyi masu zaman kansu su muna aiki tuƙuru wajen tallafawa yara su cimma burinsu, muna aiwatar da ayyukan lafiyar yara, tallafawa marayu samar da kwararrun masu horarwa wajen tsamo yara daga tallace tallace zuwa shiga makarantu”.

Dr. Zahrau ta ƙara da cewa, “Duk da ya ke ana cikin rintsi na siyasa to amma mai girma Gwamna ya ce a farantawa yara a wannan rana mai muhummanci.

“Ina tabbatar maku da cewa a wannan ofishin na wa na Maaikatar Mata ban taɓa samun tazgaro ba daga wannan gwamnatin.

“Wallahi Ganduje bai taɓa dawo da ni baya ba, kuma wani abin sha’awa Gwaggo uwa ce, to ni a lokuta da yawa ba na dosar baban sai in ta fi wajen Gwaggo nan da nan sai ka ga an sakar mana, kuma ko anan gurin ku ma shaida ne ku duba irin kudaden da gwamnati ta kashe a gurin nan”.

Ta kuma yi kira ga yara da su yi biyayya ga iyayensu inda ta ce, “ina kira gare ku da ku kula da iliminku ku yi karatu da kyau saboda ku zama manyan gobe, kuma ku samu wannan matsayi da za a rika ba ku Sifika kuna magana a gaban mai girma Gwaggo ko ma ace wata daga cikinku ne Gwaggon.”

Majalisat Ɗinkin Duniya ce dai ta ware ranar 27 ga watan Mayun kowace shekara don tunawa da wannan rana ta manyan gobe, a shekarar 1964 ne aka fara bikin wannan rana ta yara a Nigeriya inda a wannan rana yara ke bayyana irin basirar da Allah ya yi masu ta fannoni daban-daban.

Taron dai ya samu halartar Uwargidan Gwamna, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, mayan Kwamishinoni, jami’an gwamnati, hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a cikin al’umma.