COEASU ta bai wa Gwamnati wa’adin sati 6 kan buƙatunsu ko su tafi yajin aiki

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilimi (COEASU) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni shida kan ta cika alƙawarin da ta ɗauka ko kuma su tafi yajin aikin sai baba ta gani.

Mataimakin shugaban ƙungiyar ta ƙasa kuma kodinetan ƙungiyar na yankin Arewa maso Yamma, Dr. Shehu Jabaka Muhammad ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kwalejin fasaha ta tarayya ta Gusau da ke Jihar Zamfara.

Ya ci gaba da cewa, akwai buƙatar Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi taro na zagaye na biyu domin kauce wa ɗaukar matakan da masana’antu ke dauka.

Ya ce, “Majalisar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta yi duk mai yiwuwa don kawo ƙarshen yajin aikin da ake fama da shi a halin yanzu sakamakon rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da ƙungiyoyin ma’aikata a manyan makarantu’’.

A cewarsa, Gwamnatin Tarayya ta gaza magance wasu matsalolin da ke ci gaba da ruruwa a cikin shekaru da dama.

Wasu daga cikin batutuwan da Gwamnatin Tarayya ta ƙi magancewa a cewarsa sun haɗa da jajircewar dagewa kan IPPIS a kan ingantacciyar hanyar UTAS.

“Haɗin gwiwar Ma’aikata da Tsarin Bayanan Biyan Kuɗi (IPPIS) yana haifar da ɓarna ga manyan makarantun fiye da mai kyau”.

“Gwamnati ta ƙi bin buƙatar ƙungiyoyin na amincewa da tsarin fayyace gaskiya da riƙon amana na jami’ar (UTAS), madadin sabuwar ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU)”.

“Dilly-Dallying Matsayin Gwamnatin Tarayya don sake tattaunawa da COEASU-FGN 2010 Agreement yayin da aka daɗe ana tsammanin sake tattaunawa na COEASU-FGN 2010 Agreement yana da babban alƙawari don magance matsalolin da yawa da ke kawo cikas ga tsarin COE”.

Ya ci gaba da cewa, Gwamnatin Tarayya ta ki amincewa da kafa tawagarta ta sake tattaunawa bayan ta amince da karɓar jerin sunayen ƙungiyar, bisa buƙatar ta, sama da watanni biyu kenan.

Ya kuma ƙara da cewa rashin samun kuɗaɗen shiga da kwalejojin ilimi ke samu da kuma rashin ayyukan yi a fadin kwalejojin ilimi na jihar a matsayin wani babban koma-baya da ƙungiyar ke son a magance.

Ya ce, “Duk da tashe-tashen hankulan ƙungiyoyin da gwamnatoci suka dage da yin alƙawarin gyara, duka kwalejojin ilimi na tarayya da na Jihohi na ci gaba da samun ƙarancin kuɗaɗe”.

Daga nan, ya nuna rashin jin daɗinda yadda ’ya’yan ƙungiyar musamman a kwalejojin ilimi na Jihohi ke ci gaba da fama da wahalhalu na rashin biyan albashi da kuma basussukan albashi.

Dr jabaka ya bayyana cewa, “Ƙin aiwatar da tsarin albashin da aka ƙayyade gaba ɗaya, ƙa’idojin haɓakawa na ban mamaki, manufofin rashin daidaituwa, rashin / rashin dacewa cikin gida na shekaru 65 na ritaya ga ma’aikata a cikin tsarin COE”.

“Da yawa daga cikin kwalejoji na samun wahalar gudanar da aiki ba tare da wata matsala ba saboda rashin fitar da kuɗin tafiyar da su da gwamnati ta yi”.

………………………₦₦₦₦

Siyasar Kanawa a mizani

Ban ce dukka salon siyasa da Kanawa ke aiwataswa bai dace ba. Amma a fili ya ke akwai buqatuwa ga gyare-gyare tun wuri. Jihar Kano har yau ta na da tasiri ga duk wani xan takara da zai nemi kujera ta shugaban qasa. Jihar Kano ba ta da matsala ta nu na qabilanci idan magana ce ta zave ko hulxar kasuwa. Zaven 1993 wanda a kai tsakanin Marigayi Alhaji Dakta Bashir Usman Tofa na NRC, da kuma Cif MKO Abiola na SPD duk an ga Kanawa na da adalci don haka kura-kurai na zaven 2019 wanda cece-kuce ya yi ta yawo a kan zaven jiha APC da PDP a yanzu ma sai an kula tun wuri domin APC da NNPP a gefe ga PDP da PRP duka su na kartar qasa ga kujerar gwamna don haka kar ku jawo ma junanku gaba a sanadin siyasa.

Daga Mukhtar Ibrahim saulawa katsina. 07066434519/08080140820.

…………………………………….

Qaruwar adadin yaran da ba sa zuwa makaranta

A cikin watan Yunin 2013, Hukumar Kula da Ilimi, Zamantakewa da Al’adu ta Majalisar Xinkin Duniya (UNESCO), ta sanar da cewa, Nijeriya ta zama qasa mafi yawan al’umma a duniya da ke da yara miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta.

Sauran qasashen da aka bayyana sunayensu a cikin rahoton sun haxa da: Pakistan masu yara miliyan 5.1m marasa zuwa makaranta, Ethiopia 2.4, Indiya 2.3, da sauransu. A shekarar 2018, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta mayar da adadin zuwa miliyan 12.5, inda aka xora alhakin qaruwar hakan da hare-haren ta’addanci ga makarantu a Arewa. Duk da alqawarin da shugaban qasa Muhammadu Buhari ya yi na qara kuxin tallafin ilimi da kashi 50 cikin 100 nan da shekarar 2023 da kuma kashi 100 nan da shekarar 2025, alqaluman da aka samu a halin yanzu ya nuna cewa lamarin ya kau.

Akwai binciken da ke nuna cewa, daga nan har zuwa shekara ta 2030, za a cigaba da samun aaalla kashi takwas cikin 100 na qananan yara da shekarunsu suka kai shiga firamare amma ba sa zuwa makaranta a yankin kudu da hamadar Sahara.

Shugabar Asusun Kula da Ilimin Yara na Majalisar Xinkin Duniya, UNICEF, ofishin Jihar Kano, Rahama Farah, ta sanar a wata tattaunawa ta kafafen yaxa labarai kan ilimin ’ya’ya mata a qarqashin shirin UNICEF na koyar da yara mata na 3 cewa, adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya yanzu ya kai miliyan 18.5. A cikin wannan, miliyan 10 mata ne.

Nijeriya na buqatar gaba xaya sake farfaxo da harsashinta. Muna buqatar shugabanni da za su farfaxo da havaka tarbiyyar ‘ya’yanmu, musamman ‘ya’ya mata, da samar da ayyukan yi. Hakan zai rage aikata munanan laifuka a hankali tare da dawo da zaman lafiyar qasa.

’Ya’yan da muka kasa tarbiyya a yau ne za su dawo gobe su yi mana ta’addanci. Alamun sun riga sun nuna hakan!

Daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, Xalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.