Gwamnatin Jihar Zamfara ta kasa biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO

Edita, ina fatan za ka ba ni wani ɗan fili cikin wannan jarida tamu ta Blueprint Manhaja mai albarka domin na bayyana rashin jin daɗina game da gazawar gwamnatin Jihar Zamfara na kasa biyan kuɗin jarabawar kammala babbar sakandire na ɗaliban jihar wanda hukumar WAEC da NECO ke shiryawa duk shekara.

Na san mai karatu zai yi mamakin jin cewa tun shekarar 2019 zuwa har zuwa wannan shekara gwamnatin Jihar Zamfara ba ta ga dacewa da cancantar ɗaukar nauyin kuɗaɗen jarabawar yaran talakawa da ke jihar ta ba, duk kuwa da facaka da kuɗaɗen da take yi wajen neman suna da sharholiya.

A dalilin haka darajar ilimi sai ƙara komawa baya ta ke yi, bayan tarin sauran matsalolin da al’ummar jihar ke fuskanta na tsananin talauci da rashin tsaro. Babu shakka akwai abin dubawa sosai ga al’amarin da ya shafi makomar cigaban Jihar Zamfara, ba ma batun ilimi kaɗai ba. Ko da ya ke a wannan rubutun nawa matsalar ilimin ce ta fi damuna, tun da shi ne ginshiƙin cigaban kowacce al’umma.

Da yawan ‘ya’yan talakawa da ke karatu a cikin makarantun gwamnati masu ƙaramin ƙarfi ne wanda sukan dogara ne ga gwamnati a duk lokacin da aka ce ‘ya’yansu sun kai matakin ƙarshe a makarantar gaba da firamare.

Ya zama wajibi mu yi kira na musamman ga gwamnatin Jihar Zamfara tare da makusantan gwamna, da masu bata shawara ƙarƙashin jagorancin Dr Bello Muhammad Matawallen Maradun, da su dubi girman Allah su taimakawa ‘ya’yanmu da ƙannenmu a biya masu kuɗin jarabawar da suka rubuta tun da Allah ya ba wannan gwamnati damar ɗarewa a kan karagar mulkin Jihar Zamfara.

Ni dai ina da yaƙinin cewa, wannan rashin biyan kuɗaɗen jarabawar gaskiya ba ƙaramar kasawa ba ce duba da irin iƙirarin da gwamnatin ta yi, yayin yaƙin neman zaɓenta, kuma irin wannan kasawar ce tsohuwar gwamnatin Dr. Abdul’aziz Yari Abubakar, da ta gabata ita ma ta yi.

Gazawar da tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta yi musamman a ɓangaren ilimi, yana daga cikin abubuwan da wannan gwamnatin ta yi kamfen da shi kuma take iƙirarin za ta yaƙe shi a duk lokacin da Allah ya bata damar kafa gwamnati a jihar.

Shin wannan ya nuna cewa gwamnati ta gaza kenan a fannin ilmi ko kuma ta yaudari al’umma? Ko da ya ke ba lallai muna nufin gwamnati ta gaza ne baki ɗaya ba, illah dai ta yaudari jama’a ne ta wajen neman amincewarsu tare da jin cika masu alƙawari a lokacin da buƙatar hakan ta taso ba wajibin ta ba ne.

Rashin biyan kuɗaɗen jarabawar WAEC da NECO ya jawo matsaloli da dama da suka haifar da koma baya ga ilimin ‘ya’yan talakawa da suka haɗa da:

  1. Yawan zaman banza a gida, wanda babbar illa ce ga matasan mu.
  2. Disashewar ilmin ‘ya’yan talakawa masu hazaƙa.
  3. Yawon banza da shiga rigingimu masu iya jefa rayuwar su cikin haɗari.

Da haka nake kira zuwa ga gwamnati da su kansu makusantan mai girma Gwamna, malamai, ƙungiyoyin ɗalibai, sarakuna, iyaye, ‘yan kasuwa, matasa ‘yan gwagwarmaya, na wannan jiha ta Zamfara su sanya baki a kan makomar ilmin wannan jiha, a tallafi rayuwar ɗiyan talakawa don goben su ta yi kyau.

Allah ya sa wannan jan hankali ya kai inda ake so, domin duba matsalar tare da gyarata a cikin ƙanƙanin lokaci, kasancewar jihar mu na cikin jihohin da ake yi wa laƙabi da tushen arzikin noma!

Daga Isa Abdullahi Ɗanƙane, matashi ne ɗan gwagwarmaya, kuma shi ne shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers na Jihar Zamfara, +234 704 081 8166.