Kisan mace da yaranta a Anambara dabbanci ne, cewar Sarkin Musulmi

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Shugaban Majalisar Ƙoli a kan Lamurran Addinin Musulunci a Nijeriya, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya nuna damuwa akan abinda ya faru a Jihar Anambara na kisan Harira da yaran ta uku.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Mataimakin Shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo yayin wata ziyarar neman goyon bayan wakillan jam’iyyar APC da ke Sakkwato da za su kaɗa ƙuri’un zaɓen wanda zai tsayawa jam’iyyar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 wato daliget.

“Abinda ya faru a jihar Anambara, abu ne na dabbanci na kisan mace da ‘ya’yanta waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, wai saboda bambancin ƙabila ko addini, wannan abin yana nuna kamar muna yaƙi da juna ba a fagen daga ba a kafafen sada zumunta na yanar gizo, Ina son in ce idan har wannan abin haka yake.”

Bisa wannan ne dai a cewar sarkin ya yi magana da gwamnan jihar Anambara Charles Soludu da wasu jagororin yankin akan wannan batun, kuma tuni da ya gamsu da matakan da suke ɗauka na shawo kan tashe-tashen hankulan jama’a a yankin na gabashin Nijeriya don a zauna lafiya da juna.

Haka sarkin ya aminta da cewa lallai haɗin kan Nijeriya ne zai iya tsirar da ita da kuma ci gaba da riƙe martabarta a idanun ƙasashen duniya.

“Haɗin kan ƙasar nan ne ya sa take da kima a idanun duniya, kuma dole ne mu riƙe wannan martabar, kar mu yarda da duk abinda kan kawo illa ga haɗin kan mu, wannan ce hanyar da ya kamata mu zauna ƙasar nan, ƙasa wadda ke da mabambantan addinai da ƙabilu, kai ko waɗanda ba su yi imani da ko wane abin bauta ba in ‘yan Nijeriya ne dole mu zauna tare.”