Harin jirgin ƙasan Kaduna-Abuja: Mahara sun aika saƙo ga Gwamnatin Nijeriya 

Daga AMINA YUSUF ALI

Watanni biyu kenan bayan da wasu mahara suka kai wani mummunan hari ga fasinjojin jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja wanda aka kai harin Karatu ranar 28 ga watan Maris, 2022. Harin wanda aka shirya shi tsaf kafin a gudanar da shi ya yi sanadiyyar mutuwa da raunana fasinjoji da dama, da jirgin kansa da kuma ita kanta gadar jirgin. Sannan kuma uwa uba an yi garkuwa da mutane da dama. Waɗannan mutane da aka ɗauke sun shafe bikin Ista, Azumin watan Ramadan da Sallah ƙarama dukkan a hannun waɗannan ‘yan bindiga.

Kodayake, tun a kwanakin baya ne dai waɗannan mahara suka dinga wallafa bidoyo kala-kala don yin kashedi da kira ga gwamnati a kan ta cika musu wasu sharuɗɗa da ba su bayyana a bidiyon ba, kafin su saki waɗanda suke hannunsu. A yanzu bayan yin buris da su da gwamnati ta yi, sun sake aikawa da wani zazzafan saƙo ta hannun mai magana da yawun Sheikh Gumi. 

Jaridar DESERT HERALD ta rawaito cewa, a yanzu haka tana da ƙwararan hujjoji da suke nuna cewa lallai ‘yan bindigar da suka kai harin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna sun tuntuɓi mai magana da yawun Sheikh Gumi, kuma mawallafin jaridar ta Deseart Herald, Malam Tukur Mamu (Dan-Iyan Fika).

‘Yan bindigar waɗanda suka yi magana da Malam Mamu ta wayar tarho sun bayyana cewa, shi Malam Mamu shi kaɗai ne mutumin da suka amince masa a masana’antar yaɗa labarai. Sannan suka neme shi da ya isar musu saɗonsu dalla-dalla ba tare da an canza shi ba, ga gwamnatin Tarayya, iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su, da ma al’ummar Nijeriya bakiɗaya. 

A cikin saƙonnin da suka bayar ta hanyar kiran waya a lokuta daban-daban, Malam ya bayyana cewa, sun fara da bayyana cewa, a da gwamnati ta tuntuɓe su maganar sako waɗanda aka yi garkuwa da su. Amma yana tuhumar gwamnati a kan rashin gaskiya da magana ɗaya kuma hakan a cewar sa yana iya sanya rayuwar fasinjojin da suke tare da su a cikin hatsari. 

Sannan sun ƙara da cewa, gwamnatin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen ƙasan ne saboda su. Kuma idan har aka cigaba da dakatarwar, matsalar gwamnati da mutanen Nijeriya ce ba tasu ba. 

“Mu ba ma buƙatar kuɗi. Kuma muna da babban dalilin da ya sa muka aikata hakan. Kuma ina har buƙatunmu ba su biya ba, babu ɗaya daga cikin faainjojin da zai fita da ransa, ko da kuwa za mu mutu tare da su ne”. A cewar su.

“Mun zaɓe ka ne (Tukur Mamu) domin isar mana da wannan saƙo mai muhimmanci ga gwamnati, iyalan waɗanda aka yi garkuwa, da ‘yan Nijeriya gabaɗaya. Saboda mun san za ka isar mana da saƙonmu ba tare da canzawa ba. Mun sha ganin ka a dajin nan tare da Sheikh Gumi, Don haka, mun yarda da dakakkiyar zuciyarka”.

Daga ƙarshe dai shugaban tawagar wanda ya ambaci kansa da Abu Barra ya bayyana dalilinsa na yin wannan fito na fito da gwamnati shi ne, gwamnati ta qi sakar musu ‘ya’yansu da ta karve su takwas masu shekaru ɗaya zuwa bakwai. Waɗanda ya ce suna nan a gidan marayu na jimeta ta jihar Adamawa ƙarƙashin kulawar sojojin Nijeriya. Kuma a cewar sa, yanzu komai zai iya faruwa ga waɗannan fasinjojin jirgin ƙasa da suke tsare su ma a wajensa. 

Wasu daga ya’ya nasu a cewar sa su ne, Abdulrahman, Bilkisu, Usman, Ibrahim and Juwairiyyah. Kuma a cewar sa an ƙwace su ƙarfi da yaji daga hannun matansu. Sannnan kuma akwai mayaƙansu da suke a hannun sojojin Nijeriya.

Don haka, in dai gwamnati ba ta biya buqatunsu nan da kwanaki 7 ba, to za su daina kula da fasinjojin da ciyar da su. Kuma za su ci gaba da ɗaukar su ɗaya bayan ɗaya suna yankawa. Kuma sannan gwamnati ta manta da wani cigaba da amfani da jirgin ƙasan Abuja-Kaduna. Saboda ba za su taɓa bari ba. Ina dai ba a sakar musu ‘ya’yansu tare da wasu mayaƙansu da suke a kurkuku ba kuma idan aka yi ƙoƙarin kai musu hari.

Da yake mai da martani, Malam Mamu ya bayyana cewa, ya fahimci irin tsaka mai wuyar da gwamnatin Nijeriya take ciki, sai dai kuma musayar fursuna ba kanta farau ba. Hakan ya faru a wurare da dama har da Amurka. A cewar sa, gwamnati ta janye tunanin amfani da qarfin soja a wannan vangare don zai iya jawo asarar dukiyoyi da rayukan da ba su ji ba, ba su gani ba.

Mamu ya qara da cewa, sam kada gwamnati ta yi wasa da barazanar da mutanen suke yi. Domin babu lokaci. Sannan ya kamata ta gane tana magana ne da mutane bauɗaɗɗu waɗanda suke da karkatacciyar aƙida ta addini kuma waɗanda ba sa tsoron mutuwa. Don haka, ya ce a ganinsa wannan dama ce ta samu ga gwamnati don ceto waɗannan ‘yan ƙasa.


“Ni kuma a wajena idan hakan ta faru zan ji daɗin cewa waɗannan bayin Allah sun samu ‘yancinsu saboda sanya baki da na yi a ciki. Sannan a dalilin haka kuma za a samu tsaro a hanyoyin jiragen sama. Ban damu na rasa raina saboda haka ba”. Ya kamata a cewar sa gwamnati ta gane fa al’amuran tsaro suna cigaba da tavarvarewa a hanyoyin kaduna-Abuja kuma ba amfani da ƙarfin sojoji ne kaɗai maslaha ba.