Ya kamata a sanya biyan haraji a cikin sharauɗɗan tantance ‘yan takara a Nijeriya – FIRS

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar tattara haraji ta tarayyar ƙasar nan (FIRS) ta matsa lamba a kan gwamnati ta sanya biyayya wajen biyan haraji a matsayin ɗaya daga cikin sharauɗɗan tantance kowanne mai sha’awar takarar kujerun muƙamin gwamnatin ƙasar nan.

Shugaban hukumar ta  FIRS, Muhammad Nami shi ya bayyana wannan buƙata tasa a wata ganawa da suka yi da hukumar zaɓe ta Nijeriya (INEC) a ranar Talatar da ta gabata a Abuja.

Taron ganawar an yi shi ne don samun haɗin gwiwa da fahimtar juna a tsakanin wasu hukumomin tarayyar ƙasar nan. Hakazalika, hukuma mai zaman kanta ta yaƙi da rashawa da sauran Laifuka (ICPC) ita ma ta samu halartar taron. 

Shugaban hukumar FIRS, Namu ya ƙara da cewa, waɗannan hukumomi ya kamata su ƙara zage damtse wajen tsananta mutane su yi biyayya ga biyan haraji a ƙasar nan. Kuma a cewar sa, marasa biyan haraji sam bai kamata a amince da su ɗare muƙaman gwamnati don za su iya shiga dukiyar al’umma da ɓarna. Wanda bai riƙe amanar haraji ba, ina zai iya riƙe amanar dukiyar al’umma?

Sannan mariƙa muƙaman gwamnati sun ɗauki biyan haraji a matsayin abu maras muhimmanci, wanda hakan ya sa ƙarfin arzikin Nijeriya na gida (GDP) shi ne ma fi ƙarancin daga dukkan na ƙasashen Duniya. 

“Biyan haraji haƙƙi ne a kanmu kuma aikinmu ne dole mu tabbatar da duk wani ɗan ƙasa da ya cancanta ya biya harajin da a kan lokaci kuma dai-dai wa daida”. 

A cewar sa zaɓen 2023 wata dama ce da aka samu don tabbatar da biyayya ga biyan harajin. Wato a tilasta kowane mai sha’awar tsayawa takara ya bayyana shaidar biyan harajinsa a matsayin ƙa’idar cancantarsa a takarar. 

Ya ƙara da cewa, kuma a tabbatar da ‘yan takarar da ba su cika wancan sharaɗin ba, ba su samu damar wucewa neman takarar ɗarewa a kan kujerar muƙaman gwamnati ba.