MTN ya yi asarar Naira biliyan 427.44, Airtel ya zama babban kamfanin Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai kamfanin sadarwa na MTN ya samu faɗuwar wuri na gugar wuri har Naira biliyan 427.44. wannan ya ba wa abokin burminsa kamfanin Airtel dama ya zarce shi zuwa matsayin ma fi girman kamfanin a Nijeriya. 

Masu sharhi a kan al’amarin sun bayyana cewa, abin da matuƙar mamaki. Domin a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ne dai MTN ƙarfin hannun jarinsa ya yi tashin da bai taɓa yi ba a cikin makwanni 52. Wato inda ya kai kusan Naira tiriliyan shida. 

Amma sai dai hauhawar ribar ba ta yi tsawon rai ba. Domin daga nan kuma ya tafka asara har ta Naira biliyan 427.44 kwana biyu kawai a tsakani. Wannan ya faru ne sanadiyyar wasu masu hannun jari a kamfanin suka yi saurin janye hannun jarinsu saboda suna tsoron kamar hauhawar jarin ba dawwamammiya ba ce. Sanadiyyar ficewar ‘yan kasuwar shi ya haifar da wannan mummunar asarar. 

A sakamakon wannan ragas ɗin da MTN ya yi ya sa kasuwar hannun jarin ta fi ganin alamar nasara da cigaba a ɓangaren Airtel ɗin. Domin wannan faɗuwar ta MTN ta sa kuma Airtel hannun jarinsa ya ɗaga zuwa ƙarin kaso 5% wato zuwa tiriliyan Naira 5.52 a ranar Juma’ar makon da ya gabata. 

Wannan ya sa kamfanin ya zama ma fi girman kamfani a Nijeriya. Wato ma sama da kamfanin sumuntin Ɗangote wanda ƙarfin arzikinsa ya kai Naira tiriliyan 5.11.  

A yayin da kamfanin sumuntin na BUA Cement shi kuma ya zo a matsayin na 4, sai kuma kamfanin Nestle shi ya zo na biyar a jerin manyan kamfanonin Nijeriya guda biyar.