Ɓarayi sun mana ƙofar rago

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ko ta ina ka ke bi a yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya daga birnin tarayya Abuja za ka zama cikin fargabar afkawa tarkon ɓarayin mutane. Zai yi wuya a wayi gari ba ka ji an sace wani matafiyi ba. In da ma satar ce kaɗai ba tava lafiya da akwai sauƙi. Gaskiya babban makamin talakawa shi ne addu’a ko a ce neman taimakon Allah don tsarewa daga shiga waje mai hatsari.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna ta yi ƙaurin suna wajen satar mutane. Ko da bayan da ɓarayin su ka cimma burin dakatar da zirga-zirgar jirgin ƙasa da ta zama tudun mun tsira, sun koma tare hanya da sace mutane. Abin da ba za a iya dainawa ba ko da kuwa akwai barazanar gamuwa da ɓarayin shi ne bin wannan hanyar.

Haƙiƙa za ka gamu da mutane su ce ma ka ta hanyar su ka biyo kuma da yardar Allah ta nan ɗin za su sake komawa. Wannan na nuna duk matsa lambar ɓarayi ba za a bar harkokin sufurin mota ba. Allah kaɗai ya san adadin mutanen da ke hannun ɓarayin kuma su ke fatar a samu a karɓo su. Ba mamaki iya sanannun labaru irin na fasinjojin jirgin ƙasa a ka sani. Ba lalle ba ne sai fasinjoji masu bin titin ne ke halin neman agajin kuɓuta ba, za a iya samun waɗanda su ka je duba gonar su da a ka sace. Satar dai ta zama gagarumar sana’ar miyagun iri ta samun kuɗin shiga.

Ba lalle ba ne sai waɗanda ke ƙungurmin daji ne ke cin gajiyar kuɗin da a kan karɓa na fansa ba, za a iya samun hannun wasu da a ke haɗa baki da su a cikin gari ko kuma masu darewa na dajin baya ta hanyar samar da makamai da bayanai. A na zargin akwai wasu ma daga ƙetare da ke hulɗa da ɓarayin wajen ba su kayan aiki da horo.

Har yanzu ba a samu bayani filla-filla na cewa wasu jirgage masu saukar angulu da ba na gwamnati ba na sauka a dazuka da kayan buƙata na yau da kullum sannan su kwashe kuɗin da a ka tara ko ma’adinai su tashi zuwa inda ba a sani ba. An samu labarin wannan na faruwa a dazukan jihar Zamfara da Kaduna. Mun sha samun labarin jiragen jami’an tsaron Nijeriya na samun hatsari amma irin waɗannan jirage na daji ba a samun labarin gamuwa da akasi.

Hakanan hotunan da ba a tantance ba na nuna ganin wasu masu jan kunne a tsakanin miyagun irin da su ka addabi Nijeriya. Wani labarin na nuna masu ta’addanci daga gabashi na nufar yammaci da haɗa kai da ɓarayin daji. Sabon samfurin yadda ɓarayin kan nuna hotunan waɗanda su ka kama da ɓoye yanayin inda su ke na nuna sabbin dabaru.

Abin damuwar shi ne yadda za ka ga an nuna gawawwaki da sunan an rutsa da ɓarayin amma gobe sai ka ji an sake ɗauke mutane a yankin da a ka nuna gawawwakin. Hakan kan sa a rasa abun cewa. Wasu makiyaya da ke daji na kokawa da cewa su ma varayin na kai mu su hari kuma ba lalle ne a iya tantance su da miyagun irin ba.

Irin wannan misalin ya faru a yankin Chikun yayin da wasu makiyaya su ka ci karo da ‘yan banga alhali su ma su na neman ɓarayin shanun su ne. Rahoto ya nuna nan a ka yi mu su rotse da mika su hannun jami’ai su kuma su ka riƙa loda su a mota tamkar shanu ko ma ita ce. A sanadiyyar haka kafin gane gaskiyar lamarin wasu sun rasa ran su. Aiki da fasahar tsaro da dabarun yaƙi na da muhimmanci don kar a zalunci wanda ba shi da laifi sannan a samu nasarar magance asalin masu laifin.

Duk dazukan da a kan samu miyagun iri na fakewa sanannu ne kuma tabbas za a iya ganin su ta na’ura. Kazalika amfani da na’urorin ta hannun ƙwararru shi ne mafi a’ala. Baya ga ƙwararrun ya zama an samu masu amana da aiki don kishin samar da tsaro ga al’umma. A kan samu kuskure a wasu lokutan inda hatta harin jirgin sama ka iya faɗawa kan mutanen kirki na banza su tsira.

Yanzu in ka yi misali da dajin Birnin Gwari za ka ji labaru masu sabawa juna cewa ainihin inda miyagun su ke zama ba a iya zuwa. Kuma har da wajajen zama masu ma’ana da majalisun hira da sadarwa har ma da jami’an tsaron cikin miyagun iri da a kan ajiye don kare yankunan da ankarar da gaggan varayin da zarar an hango jami’an tsaron gwamnati na tinkarowa.

Ba ta yadda za a yi a ce a bankawa daji wuta gaba ɗaya don gari ba ya rayuwa sai da daji. Albarkatun da ke daji na da yawa kama daga dabbobi, bishiyoyi, ma’adinai da ma sauran ‘yan ƙasa da sana’ar su ke gudana kacokan a ƙungurmin daji. Hakan ya nuna sai an samu labarun sirri kafin kai hari.

A wasu hotunan bidiyo a na ganin jami’an tsaro na ɗaukar matakan da su ka wuce gona da iri kamar barar da albarusai ga gawar wanda tuni ya riga mu gidan gaskiya da furta kalamai na ashar da a ƙarshe kan haddasa saɓani da nasara.

Kusan duk hanyoyin da a baya a ke ɗauka su na da tsaro yanzu lamarin ba haka ya ke ba. Ka ga hanyar Abuja zuwa arewa maso gabar ta Akwanga fitacciyar hanya ce da ba ta da tarihin matsala sosai. Sace shugaban ƙaramar hukumar Keffi Muhammad Baba Shehu a daf da garin Gude na nuna ta’azzarar satar mutanen da kan nausa yankunan da ba a tsammanin hakan. Ba ma kawai sace shugaban ƙaramar hukumar da mai tuƙa motar sa ba, ɓarayin wadanda yara ne sun yi kisan gilla ga ɗan sandan da ke tsaron lafiyarsa Sajan Alhassan. Ba vata lokaci ɓarayin su ka nemi kuɗin fansa Naira miliyan 30.

Allah ya kuɓutar da shugaban ƙaramar hukumar da abokin tafiyarsa amma sun ji jiki sosai da rahotanni su ka nuna an ma kwatar da su a asibiti. Barayin dai yara ne da ba su san darajar ran ɗan adam ba in ka ɗebe kuɗi da su ke buƙata. Majiya ta bayyana min cewa lokacin da su ka bugo waya don neman kuɗin fansa har haƙuri su ka bayar kan kisan gilla da su ka yi wa Sajan Alhassan cewa kamar ba da gangan su ka yi ba; sun ga jami’in tsaro ne shi ya sa su ka yi mugun halin na su.

Hanyoyin da ɓarayin kan tare mutane akasari na manyan hanyoyin tarayya ne da ba a rasa su da jama’a masu zirga-zirga dare da rana. Fargabar gamuwa da ɓarayi ko a da can ’yan fashi da makami ba ya hana mutane bin hanya don rayuwa ba za ta yiwu cikin nasara ba sai da motsawar mutane da kadarorinsu. Hakan ya sa ya zama mai muhimmancin gaske sanya jami’an tsaro kan manyan hanyoyi da za su riƙa sintiri ba ya ga kafa madakatun mota. Ka ga za a riƙa samun sadarwa tsakanin jami’an tsaron da ke sintiri da kuma waɗanda ke madakatun ta inda za a iya ɗaukar mataki da zarar an ji labarin bayyanar miyagun iri. Ba na tsammani miyagun irin nan sun fi ƙarfin jami’an tsaro.

Ya na da kyau a samawa jami’an tsaron hasafin aiki da makamai nagari da cusa mu su aƙidar kishin ƙasa ta yadda ba za a riƙa samun baragurbi a cikinsu ba. Haƙiƙa matuƙar a ka tsame ɓata-gari ko wake ɗaya kan ɓata miya a tsakanin jami’an tsaro, za a iya cimma burin samar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.

Akwai zullumi da matuƙar takaici a riƙa samun tsoro a tsakanin jama’a ta yadda tafiya ɗaga wannan gari zuwa wancan ya zama tamkar sayar da rai don yadda hakan ya ke da hatsari. To ina ma amfanin ka na tafiyar ka, ba ka tsokani kowa ba ka saba kowace doka ba, sai wasu kawai sun fito daga dajin da ba ma na su ba ne su yi ma ka barazana matuƙar ba ka ba su maƙudan kuɗi ba? Kazalika a yau in tsautsayi ya gitta a ka ɗauke ma ka dan uwa to sai dai kai da dangin ka kusan yadda za ku kukuta wajen karɓo ɗan uwan ku amma ba wani tallafi da zai zo daga hukuma. Ba ma tallafi ba zai yi wuya ko jajantawa a samu kuma ga ƙarfafa batun nan na sai in an daina biyan kuɗin fansa ne kaɗai za a samu sauƙin wannan mugun yanayi.

Kammalawa:
Yaƙi da ɓarayin nan na buƙatar ɗaukar matakan a ciza a hura ta hanyar fito na fito da kuma gano matsalolin waɗanda su ka bijire don magance hakan. Da alamun za a iya kwance damarar ginshiƙan miyagun da su kuma za su hana sauran muƙarraban su cigaba da fakewa a daji don cutar da jama’a. Idan buɗe wuta kaɗai na iya kawo ƙarshen fitina, da yau ba za a sake jin ɗuriyar ’yan ta’adda a Arewa maso Gabas ba.