Okorocha ya bayyana wajen tantance ‘yan takara jim kaɗan bayan samun beli

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Gwmanan Jihar Imo kuma ɗan takarar Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, ya bayyana gaban kwamitin tantance ‘yan takarar Shugaban Ƙasa ranar Talata da daddare a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja domin a tantace shi.

A makon da ya gabata ne Okorocha ya faɗa a komar EFCC bisa tuhumar almundahana na biliyan N2.9.

Tsohon gwamnan na daga cikin ‘yan takarar da ke zawarcin shugabancin Nijeriya ƙarƙashin Jam’iyyar APC a 2023.

By Editor