Tir da kisan gillar ’yan Arewa a Kudu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ina wannan rubutu ne zuciyata cike da ƙunci da ɓacin rai game da kisan gillar da aka yi wa wata mata ’yar Arewa mai suna Harira Jibrin da ke ɗauke da tsohon ciki, tare da yaran ta huɗu, Fatima, Khadija, Hadiza da Zaituna, a yayin da suke kan hanyar su ta komawa gida daga wata ziyara da ta kai wa wata ’yar uwar mijinta a yankin Isulo da ke ƙaramar hukumar Orumba ta Kudu a Jihar Anambra, a ranar Litinin da ta gabata.

A wani gajeren bidiyo da ke yawo a zaurukan sada zumunta na yanar gizo, an nuna marigayiyar kwance cikin jini a titi, kusa da ita gawarwakin yaran nata 4 duk mata, su ma an yi musu yankan rago. Subhanallah.

Wannan abin baqin ciki ne da ɗaga hankali matuqa, ba gare ni ba ko ’yan Arewa kaɗai ba, duk wani ɗan Adam mai hankali da ya kalli wannan mummunan aika-aika tilas hankalinsa ya tashi, zuciyarsa ta harzuƙa, don ganin yadda ‘yan Kudu, musamman ‘yan ƙabilar Ibo ke cigaba da yi wa ‘yan uwanmu ‘yan Arewa kisan gilla da ƙona dukiyoyin su, ba laifin tsaye ba na zaune, don kawai su Hausawa ne ko ‘yan Arewa.

Ba tun yau ba, ‘yan Arewa mazauna yankin kudancin Nijeriya ke kokawa game da yadda ake yi musu wulaƙanci da kisan gilla, da takura musu wajen gudanar da ayyukansu, da rusa musu wuraren su na kasuwanci da wuraren ibada, duk kuwa da yadda kafafen watsa labarai mallakar ‘yan Kudu ke ɓoye wasu labaran abubuwan da ke faruwa, yayin da kashe-kashe ke qara tsananta.

Ƙungiyoyin tsagerun matasa masu ɗauke da makamai da na ‘yan ƙungiyar neman ɓallewar ƙasar Biyafara daga Nijeriya, sun daɗe suna cin karensu babu babbaka, suna kashe mutane da ƙone motocin dakon kayan abinci da ake kaiwa jihohin Kudu daga nan Arewa da gayya ba tare da tunanin wani abu zai faru ba, saboda sun san da zarar magana ta tashi za a ce ’yan Arewa su yi haƙuri kar a tada fitina.

Ko a ƙarshen makon da ya gabata ma sai da wasu tsagerun matasa suka tare wasu manyan motocin ɗaukar kaya a Jihar Anambra, suka kuma kashe dukkan mutanen da ke ciki. Ba tare da an ce wani abu ba ko an kama wasu an gurfanar da su gaban hukuma ba. Haka abin yake a sauran jihohin Inyamurai irin su Inugu, Imo, da Ebonyi, har ma da maƙwabtansu irin su Delta.

Malama Nana Basira Musa da aka fi sani da Maman Fadila ’yar asalin Jihar Sakkwato ce da yanzu aure ya kai ta Warri da ke Jihar Delta kuma take zaune tsawon shekaru 13, ta yi matuƙar kokawa da halin rayuwar da ‘yan Arewa ke ciki, na rashin ’yanci, rashin tsaro da rashin ƙwaƙƙwaran shugabannin da za su tsaya domin kare haƙƙoƙin ‘yan Arewa da ke rayuwa a jihohin kudancin ƙasar nan, musamman a jihohin shiyyar kudu maso gabashin ƙasar nan.

Ta yi takaicin yadda ‘yan ta’adda da tsagerun matasa na ƙungiyoyin asiri ke cin zarafin matasan Arewa masu zuwa Kudu cirani da ayyukan neman na kansu, idan sun fito ayyukan su na ta’addanci babu babba ba yaro, in dai kai ba nasu ba ne. Kamar yadda ta ce ko da a lokacin ƙaramar Sallah da ta gabata sai da aka jibge jami’an tsaro sosai, kafin aka samu aka hau idi. Washegarin Sallah kuwa haka suka fita suna harbi da kisa kan mai uwa da wabi.

Shima Nafi’u Usman Doma ɗan Jihar Filato da ke aikin tuƙa Keke Napep ko A Daidaita Sahu a garin Inugu, ya bayyana cewa gaskiya rayuwar babu daɗi, sakamakon yadda ‘yan ƙungiyar IPOB ta ‘yan tawayen Biyafara suke cin mutuncin ‘yan Arewa. Ya ce, “a gaskiya muna zaune cikin tsoro da fargaba, ba ko’ina ‘yan Arewa ke iya shiga su yi aiki ba, saboda tsoron za a iya yi musu kisan gilla”. A cewar sa ko a makon da ya gabata ma wani ɗan uwansa da ke aikin Keke Napep da ƙyar ya tsira da ransa, yayin da aka tafi da Keke Napep ɗin.

Ya kuma yi zargin cewa, jami’an ‘yan sanda da ya kamata su tsare rayuwar mutane babu abin da suke iya yi, akasarin su ma bakin su ɗaya da ‘yan IPOB xin, sai dai a inda ka yi sa’a da jami’in tsaro ɗan Arewa. Kaico, lamari ya lalace.

A wata takardar da ƙungiyar IPOB ta fita kuma aka raba wa manema labarai mai ɗauke da sa hannun Kakakin ƙungiyar Emma Poweful, ƙungiyar ta nisanta kanta da kisan gillar da aka yi a Jihar Anambra, inda ta ce babu inda ƙungiyar ke goyon bayan afkawa ‘yan Arewa ko kasuwancinsu, kuma za ta binciko waɗanda suka yi wannan ɗanyen aikin. Shi ma madugun haramtacciyar ƙungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu da ke tsare a hannun jami’an tsaron DSS, an ruwaito ya aika wa ‘yan ƙungiyar su guji tava ‘yan Arewa, kuma lallai a kamo waɗanda suka yi wa Malama Harira da yaranta huɗu kisan gilla, don a hukunta su.

Sai dai, shin waɗannan maganganu ne na siyasa kawai ko kuma wani sabon salon yaƙi da ‘yan Arewa ne. Nafi’u Usman Doma da ke zaune a Inugu dai ya ce, wannan zancen banza ne, domin kuwa duk barnar da ake yi wa ‘yan Arewa a jihohin Inyamurai yaran IPOB ne suke aikatawa, ba sa ma ɓoye kansu. In dai kai ɗan Arewa ne kawai ka shiga uku!

Bisa ga dukkan alamu yanzu dai tura ta fara kaiwa bango, matasan Arewa da suke jin zafin abubuwan da ke faruwa da ‘yan uwansu a jihohin kudancin ƙasar nan, sun fito da kausasan kalamai ƙarƙashin Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa ta Coalition of Northern Groups, inda a ta bakin Kakakin ƙungiyar Abdul-Aziz Suleiman, ƙungiyar ta ɗora alhakin abubuwan da ke faruwa kan ‘yan Arewa a Kudu, kan irin baƙaƙen kalamai da aibata ‘yan Arewa da shugabannnin al’ummar yankin suke yi wanda hakan ke angiza matasan suna abin da suka ga dama na kisan gilla da ta’addanci.

Sannan ƙungiyar ta kuma yi gargaɗin cewa, idan har aka kasa yin wani abu a kan wannan mummunan aika aika ‘yan Arewa za su ɗauki matakin ƙauracewa saye da sayarwa tsakanin su da ‘yan Kudu da kuma ƙaurace wa kafafen watsa labaransu, waɗanda a duk lokacin da wani abu ya shafi ɗan kudu ko wanda ba Musulmi ba a Arewa sai su yi ta kururutawa, amma komai munin abin da ya shafi ‘yan Arewa a Kudu, sai su kawar da kai kamar ma ba abin da ya faru. Ba yau ne jaridun Kudu ke yin irin wannan hali ba, kusan a kowanne lokaci aka samu matsala a tsakanin yankin Arewa da Kudu, ‘yan Kudu kan yi wa Arewa taron dangi ne ta kowanne ɓangare, saboda lura da gazawar ‘yan Arewa wajen haɗa kansu da magana da murya ɗaya, ko amfani da kafafen watsa labarai yadda ya dace.

Alhaji Ibrahim Abdullahi Ibzar ɗan kasuwa mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, na ganin lallai sai gwamnati ta tashi a tsaye ta ɗauki mataki kan irin waɗannan abubuwan, idan ba haka ba, a sannu a hankali za a riqa kunna wutar da za ta iya mamaye ƙasar nan, kowanne ɓangare ya ɗauki makamin kare kansa, a riqa farautar juna. Rikicin ƙabilanci da na addini ba zai yi wa ƙasar nan kyau ba, a cewar sa. ‘Lallai bai kamata ana barin matsala tun tana ƙarama har sai ta zama ta gagari jami’an tsaron mu ba. Abin da ya ke faruwa a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma ya kamata ya zama mana darasi.’

A rubutuna na makon jiya, mai taken ‘Hattara da masu son raba kan ‘yan Nijeriya’ na tavo wasu daga cikin waɗannan matsaloli da na ja hankalin ‘yan Nijeriya game da abubuwan da za su yi ta faruwa, a wannan lokaci da ‘yan ƙasa ke shirye shiryen tunkarar Babban Zaɓen 2023. Amma duk da haka ‘yan Arewa ba za su naɗe hannu suna gani ana wulaƙanta ‘yan uwansu da tozarta musu rayuwa da sunan haɗin kan ƙasa ba. Dole ne shugabannin yankin su fito su tsawatar kan wannan ta’addanci da ake yi wa ‘yan Arewa a jihohin su ba dare ba rana, kuma su tabbatar an hukunta waɗanda suka yi wa Harira da yaranta 4, da sauran al’ummar Arewa da ake yi wa kisan gilla.

Hotunan bidiyo da suke fitowa daga jihohin ‘yanƙabila Ibo, suna da matuƙar ɗaga hankali da tsoratarwa matuƙa. Sai dai duk da haka muna kira ga ‘yan Arewa a guji ɗaukar doka a hannu, kada wasu su ce za su ɗauki mataki don kashe Inyamurai a Arewa ko lalata dukiyoyinsu da wuraren su na kasuwanci, ba lallai ne mu yi yadda suka yi mana ba. Amma yin shiru da kawar da kai ba namu ba ne, dole ne mu buɗe baki mu yi magana, a kafafen yaɗa labarai daban-daban, mu yi amfani da duk wata dama da kundin tsarin mulkin ƙasa ba mu, don mu nuna rashin amincewar mu da wannan ɗanyen aiki.

Sannan, ina mai ba da shawara ga ‘yan kasuwar Arewa, da masu dakon kayan abinci da dabbobi zuwa Kudu ko zuwa sayayyar kayayyaki su yi haƙuri su jinkirta kaɗan har abubuwa su lafa tukunna, su daina kai kansu halaka da sunan neman kuɗi, su ma waɗanda ke zaune a can su yi hattara da wuraren da za su shiga, don tsira da rayuwar su.

Ya zama dole a yi takatsantsan wajen tunkarar waɗannan matsaloli waɗanda za su iya haifar da ƙarin rabuwar kai a tsakanin ‘yan Nijeriya, kuma ya haddasa ƙalubale masu a harkokin Babban Zaɓen da ke tafe. Taɓarɓarewar tsaro a yankin jihohin Kudu maso Gabas da Arewa maso Gabas, da ɓangaren Arewa maso Yamma abin tashin hankali ne matuƙa ga cigaban haɗin kan ƙasar nan da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya.

Jawabin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari game da kisan gillar da ake yi wa ‘yan Arewa da ya bayyana a matsayin “masu matuƙar ɗaga hankali”, tare da gargaɗin masu aikata hakan da cewa su tsammaci tsattsauran martani daga jami’an tsaro, bai wadatar ba gaskiya, lallai muna zuba ido mu ga matakin da Gwamnatin Tarayya da Majalisar Gwamnonin Arewa, Majalisar Ƙasa, da manyan ‘yan siyasar Arewa waɗanda yanzu batun zavukan fitar da gwani ne ya fi ɗaukar hankalin su, za su ɗauka, don ganin an ƙwatowa Harira da yaranta da sauran ‘yan Arewa haƙƙoƙinsu, domin a samu kwanciyar hankali a zaɓe lafiya.