Badaƙalar biliyan N200: Akanta Janar ya bayyana sunayen wasu a matsayin waɗanda ake zargi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Badaƙalar da ta shafi Akanta Janar na Tarayyar Nijeriya da aka dakatar, Ahmed Idris na iya cinye wasu jami’an gwamnati yayin da Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta tsananta bincike.

Rahotanni sun bayyana cewa, bisa sakamakon binciken da hukumar EFCC ta gudanar, jimillar kuɗaɗen da aka samu a cikin jerin badaƙalar hada-hadar kuɗaɗe da aka dakatar da Akanta Janar akansu ta kai Naira Biliyan 200 (N200,000,000,000).

Idan za a iya tunawa cewa, jami’an EFCC sun kama Idris ne a ranar 16 ga Mayu, 2022 kan wasu zamba da aka fara tunanin Naira biliyan 80 ne.

Kwanaki uku bayan kama Idris, ministar kuɗi, kasafin kuɗi da tsare-tsare ta ƙasa, Zainab Ahmed ta dakatar da Idris domin a bincike sa.

Wanda ake zargin ya yi ikirari, kuma ya bayar da bayanan kuɗaɗe, cirewa da kuma ajiyar kuɗaɗe a cikin gida da waje.

An ce hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, a makon da ya gabata, sakamakon alaƙarsa da Akanta Jana, kuna har yanzu yana tsare.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kuma damƙe shugaba kuma Manajan Daraktan Finex Professional, Anthony Yaro.

Wasu daga cikin laifukan da ake zargin sun faru ne a lokacin da Nwabuoku ke riƙe da muƙamin Daraktan kuɗi da asusu na ma’aikatar tsaro.

Wani kuma da ake zargin an tafka damfara ta hanyar gwamnatin haɗaka da hada-hadar kuɗi (GIFMIS) da ake amfani da ita wajen biyan albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya.