Na fuskanci ƙalubalai bayan mutuwar mijina – Hajiya Ramlat Buhari

“Burina rayuwata ta amfanar da wasu”

Hajiya Ramlat A. Buhari da wasu ke kira da Hajiya Laure, mace ce mai kamar maza, ‘yar kasuwa, ‘yar jarida, marubuciya, malama, mai kishin ilimi da taimakon raunananu. Ta taso a garin Jos cikin gata da kyakkyawar tarbiyya, daga bisani rayuwa ta yi mata juyin masa, sakamakon rasuwar mijinta, wanda rasuwar sa ya sauya mata rayuwa bakiɗaya. Ta yi fama da raino da tarbiyyar yara marayu da aka bar ta da su, don su zama mutane nagari, sannan ita kanta ta koma makaranta, don kishin da take da shi na samun ilimi, inda ta yi karatu a Kwalejin Talabijin ta NTA dake Jos, saboda burin da take da shi na ba da gudunmawa a cikin al’umma. Ta kasance marubuciyar littattafan faɗakarwa, da take rabawa, don ƙaruwar al’umma maza da mata. Wakilin Manhaja a Jos, ya samu zantawa da Hajiya Ramlat, don jin darasin da rayuwarta za ta koyarwa masu karatu.

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

MANHAJA: Wacce ce Hajiya Ramlat A. Buhari?
HAJIYA RAMLAT: Hajiya Ramlat A. Buhari wata baiwar Allah ce kainuwa dashen Allah. Asalin iyayena ýan Jihar Kano ne, amma zama ya kai babana garin Jos a Jihar Filato, inda ya ke gudanar da harkokin sa na kasuwanci. A can aka haife ni da sauran ýan uwana har na yi karatun allo da na boko. Na yi Diploma a kan aikin jarida vangaren talabijin, sannan kuma bayan komawa ta Kano da zama na ci gaba da karatu a Kwalejin Sa’adatu Rimi, inda na yi karatu a fannin nazarin harshen Turanci. Ni mace ce mai son karatu da ba da ilimi, a duk inda na samu kaina.

Yaya rayuwarki ta kasance a lokacin tasowarki?
Na taso a babban gida, ba ina nufin gida mai tarin jama’a ba, a’a gidan dattijan ƙwarai, jinin sarauta, kuma malamai. An sa mu a harkar neman ilimi na addini da na boko, don haka mun taso da ƙishir ruwan ilimi, kuma har yanzu a cikin sa muke. Na taso ina da son kwalliya da tsafta, tun ina yarinya bana son ƙazanta. Ina da ƙyama, ba na son wari, har yanzu ma ina son ƙamshi kuma alhamdulillah, wasu ma idan sun ganni ba sa yarda ni na haifi ‘ya’yana, saboda yanayin jikina.

Wacce gwagwarmaya kika sha wajen neman ilimi?
To, ina ƙarama dai ban samu wata matsala a tasowa ta ba, don kamar yadda na faɗa a baya, mahaifinmu mutum ne tsayayye a kan ilimi, bayan na gama sakandire aka yi min auren fari. Bayan rasuwar mijina na sake komawa karatu, na yi satifiket a kan sarrafa na’urar kwamfiyuta, sannan na yi Diploma a fannin aikin jarida. Na shiga Jami’ar Bayero ta Kano don in yi Digiri na na farko a fannin aikin jarida, amma ban yi nisa sosai ba, yarana da muke karatu tare da su a nan BUK sai suka hana ni, don ba sa son a ce suna zuwa karatu tare da mamansu. Dalili kenan da ya sa na koma Kwalejin Sa’adatu Rimi.
Babu shakka na sha gwagwarmaya da fuskantar ƙalubale iri-iri, musamman a lokacin da yarana ke ƙanana, ga nauyin kula da gida, don na gaya maka mijina ya rasu ya bar ni da ƙananan yara biyar, huɗu mata ɗaya namiji. Ni zan shirya su in kai su makaranta, sannan nima in wuce tawa makarantar, cikin ƙunci da gajiya da yunwa. Ga shi lokacin mata ba su gane fita neman ilimin boko sosai ba, mu ýan kaɗan ɗin da muka fita nema mun haɗu da maganganu iri-iri. Amma yanzu mun zama abin sha’awa, kuma abin koyi ga kowa.

Na ji kin yi karatun aikin jarida. Shin kin yi aiki a wata kafar watsa labarai ne?
E, haka ne. Na daɗe ina sha’awar aikin jarida. Ina son gabatar da shirye shirye ko shirin hirarraki da baƙi. Amma Allah bai nufa na yi aikin jarida ba, har yanzu. Sai dai lokacin da muna makaranta, mun je aikin sanin makama na wasu watanni a tashar talabijin ta NTA Jos. Amma in sha Allahu ina da burin nan gaba kaɗan zan buɗe tashar talabijin ta kaina, domin kara faɗaɗa ayyukan wayar da kan jama’a kan sha’anin addini da tarbiyya.

Mu je ga batun rubuce rubucen ki, an ce kina buga littattafai?
E, babu shakka. Na yi rubuce rubuce na ƙananan littattafan faɗakarwa da suka shafi zaman iyali, tarbiyya da wasu ayyuka na addini. Kawo yanzu dai ina ganin na rubuta littattafai za su kai kamar 26. Sha’awata da rubuce-rubucen littattafai ya samo asali ne daga mu’mallah da labaran mutane iri-iri, na tausayi, rashin sani, abin haushi. Sannan kuma ga shi wasu mutane ba kasafai suke iya cire kuɗi don sayen littafin da za su amfani rayuwar su da shi ba. Shi ya sa nake rubuta waɗannan littattafai ina rabawa musamman a kowanne watan Ramadan kuma kyauta nake bayarwa wuraren tafsirai. Tun ina buga kwafi dubu ɗaya, har yanzu sai mu yi dubu huɗu ko biyar, wasu ma suna karɓar suna ƙara bugawa da kuɗin su, don amfanin al’umma.

Wacce gudunmawa kika bayar ga cigaban al’umma da damar da kika samu?
To, ni a tsarin rayuwata ban cika bayyana ayyukan da na yi wa wani saboda girman Allah ba. Ni dai abin da na sani komai na wa na al’umma ne. Duk inda na ga akwai buƙatar taimakawa don samun lada mai gudana wato sadaƙatul jariya, ina nan a wajen kama daga kan ciyarwa, suturtawa, tallafin sana’a, riƙon iyali, kula da marayu da raunana. Tallafa wa ýan fursuna masu zaman gidan gyaran hali, gina wuraren ibada da sauran ayyukan addini. Na riƙe wasu yara da suka girma a ƙarƙashin kulawata har suka girma suka yi karatu, na yi musu aure. Alhamdulillahi.
Ayyukan an yi su suna nan da yawa, sai dai su waɗanda aka yi wa abin sun sani, sai kuma Allah Madaukakin Sarki da aka yi aikin saboda shi.

A yanzu waɗanne harkoki ne kika shagaltu da su don amfanin jama’a?
To, Alhamdulillahi. Ina nan kan abin da na saba. Ina kula tarbiyyar iyalina da ta jama’a da dama. Ina kuma taimaka wa ma’aurata da shawarwari na yadda za a inganta zaman aure. Haka kuma sauran ayyuka na taimaka wa al’umma yana nan ana ci gaba da taimaka wa a ko da yaushe. Burina dai shi ne wani ya ji daɗi ko ya samu kwanciyar hankali ta dalilina.

Wacce shawara za ki bai wa matan da suka rasa mazajensu aka bar su riƙon yara?
To, agaskiya shawarata da zan bai wa iyayen marayu shine su sha ɗamara ta wajen kula da ‘ya’yansu su rabu da maganar sake sabon aure da wuri, su jajirce ta wajen kula da neman ilimin su na addini, da na zamani. Su kula da su ta wajen koya musu tarbiyya, kula da tsaftar jikinsu, kalmomin su. su san darajar mutane su gane wannan babba ne wannan ƙarami ne, sa’a na ne, malamina da sauran su. A nuna musu mihimmacin karatu kar a ce yara ne, a riƙa ba su littattafai na yara suna karanta su suna kara su tashi da sanin harshen Turanci da Larabci. Za su tashi da basira, ba shirme ko gulmace-gulmace, da wasa mara ma’ana ba. Sai kuma uwa uba, a tsananta yi musu addu’a a ko da yaushe.

Da wanne abu kike so a riƙa tunawa da ke?
Da littattafai na da wasu ayyukan da na yi, wanda wannan kuma sirri ne tsakanina da Allah da wanda ya shafe su.

Na gode.
Ni ma na gode ƙwarai da gaske.