Iyalai sun koka kan shirun mahukunta mako guda bayan turmutsutsin gidan gwamnatin Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Bayan sati ɗaya da turmutsutsin gidan gwamnatin Jihar Neja da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku da raunata wasu da dama, gwamnatin jihar da rundunar ‘yan sanda sun cigaba da kasancewa a halin abin da iyalai suka kira da “halin ko-in-kula” kan al’amarin. Sun bayyana damuwa kan yadda babu wani saƙo ko ta’aziyya a hukumance daga bangarorin biyu kan waɗanda suka rasu a iftila’in ko kuma samar da wani tallafi ga iyalan mamatan.

Manhaja ta ruwaito cewa, Gwamnatin Jihar Neja zuwa yanzu ba ta fitar da wani bayani ba a hukumance game da aukuwar lamarin na ranar 29 ga Satumba, 2026 a gidan gwamnatin da ke Minna duk da tabbacin fitar da sanarwar da fari da aka yi musu. Bologi Ibrahim, wanda shi ne sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Mohammed Umaru Bago jim-kaɗan bayan aukuwar iftila’in, ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta fitar da sanarwa a kai “a lokacin da ya dace”.

Kamar haka ita ma Rundunar ‘Yan sandan Neja ba ta fitar da wani gamsashshen sako ba. Da fari kakakinta, SP Wasiu Abiodun ya ce rundunar za ta tantance rahotannin sannan da bayar da amsa a kai daga bisani, amma har yanzu shuru babu wani bayani.

Mako guda da ya gabata ne mutum uku suka rasu a lokacin da ake rige-rigen karɓar tallafi a gidan gwamnatin yayin da wasu suka jikkata, waɗanda suna cigaba da karɓar magani a Babban Asibitin Minna. Al’amarin ya auku ne a ranar Talata a lokacin da aka yi zargin an gayyaci wasu matasa da nufin lallashin su bayan sun shirya gudanar da zanga-zangar mutuwar masu aikin haƙar ma’adinai na gargajiya guda 37 a ofishin hukumar Sibil Difens (NSCDC) da ke jihar.

An ruwaito cewa, kasancewar an samu yaɗuwar labarin da ke cewa gwamnan zai raba kuɗi ga waɗanda suka je gidan, an samu ƙarin wasu dandazon jama’a ciki har da mata. Daga cikin waɗanda suka rasu akwai wata mata mai suna Dije da ‘yarta Hurairat, waɗanda ‘yan gudun hijira ne daga ƙauyen Allawa da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro. Mijin Hurairat, Abubakar, wanda shi kuma mahauci ne, ‘yan bindiga sun halaka shi tun a shekarar 2023 akan hanyar Allawa zuwa Pandogari.

Da yake ganawa da manema labarai, ɗan uwan ɗaya daga cikin mamatan mai suna Malam Auwalu, ya yi tir da matakin gwamnati na yin shuru game da al’amarin, inda ya ce iyalan suna ɗaukar hakan a matsayin an yi watsi da su saboda waɗanda suka rasu marasa galihu ko ‘yan gudun hijira ne. Ya bayyana cewa, hakan ya ƙara sanya su a halin jin cewa ba za a musu adalci ba kan waɗanda suka rasu, yana mai cewa za su bar al’amarin ga Allah, wanda shi zai yi hukuncin ƙarshe a kai.

By Babaji

Leave a Reply